Sulaiman Ibrahim">

Masu Garkuwa Sun Sace Malami Da ‘Ya’yansa A Kwalejin Nuhu Bamalli Ta Zariya

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun mamaye makarantar kimiyya ta Nuhu Bamalli da ke garin Zariya, jihar Kaduna, inda suka yi garkuwa da malami da ‘ya’yansa.

Lamarin, wanda ya faru a daren Asabar, ya faru ne yayin da dalibai ke komawa makaranta don cigaba da karatu bayan kulle ta da akayi sanadiyyar Cutar Korona.

Shugaban makarantar, Kabir Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce ‘yan bindigar sun samu damar shiga makarantar ne da misalin karfe 9 na dare.

Abdullahi ya ce an sace daya daga cikin malaman tare da yaransa biyu.

Ya bayyana sunan malamin da Bello Atiku, wanda kuma shi ne Shugaban Sashin Kimiyyar Kwamfuta na makarantar.

Shugaban ya kara da cewa an harbi wani ma’aikacin makarantar, Sanusi Hassan a hannu kuma da kyar ya kubuta daga hannun masu garkuwar. Amma an gaggauta kai shi asibiti don kula da lafiyarsa.

Shugaban ya ce, “Ina Kaduna lokacin da Babban Jami’in Tsaro na kwalejin ya kira ni ya sanar da ni game da harin.

“Gaskiya ne cewa wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun sace daya daga cikin ma’aikata na, Injiniya Bello Atiku wanda shi ne Shugaban Sashen, kimiyyar kwamfuta na makarantar.

“An sace shi tare da yaransa biyu zuwa wani wurin da ba a san ina bane”

Exit mobile version