Masu Goyon Bayan Ta Da Fitina A Yankin Yarbawa Wawaye Ne- Aregbasola

Aregbasola

Daga Rabiu Ali Indabawa

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola a ranar Asabar ya ce wadanda ke jagorantar da kuma goyon bayan ta da hankali ga kasar Yarbawa wawaye ne yana cewa “ya kamata su yi la’akari da sakamakon yaki ke haifarwa.”

Aregbesola yayin da yake magana a Otal din Zenabab, Ilesha, Jihar Osun yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekara 64, ya yi gargadin cewa masu son tayar da zaune tsaye dole ne su yi la’akari da mata, yara kanana, tsofaffi da wadanda ke fama da nakasa wadanda galibi abin ya shafa.

Ya ce dole ne Nijeriya ta kara hadewa waje guda idan kasashen Afirka za su sake zama bayi. Ya lura cewa Nijeriya ita ce kasar da za ta ‘yantar da Afirka daga duk wata danniya saboda haka kada ‘yan Nijeriya su yarda da masu ra’ayin ballewa.

Ya kara da cewa “Duk wani abin da ke barazana da haifar da matsala ga Nijeriya na iya haifar da koma-baya ga kasarmu tsawon shekaru 50,”

Exit mobile version