Yawan wadanda suka bukaci bashin hakar ma’adanai na gwamnatin tarayya a fadin kasar nan na naira biliyan 14.6 sun kai guda 138. A ranar Talata ce, aka bayyana cewa, wadanda suke bukatar amsar wannan bashi na naira biliyan 14.6, wanda bashi ne da asusun hakar ma’adanar na biliyan biyar yake bai wa masu hakar ma’adanai, wanda aka samar a shekarar 2017 karkashin ma’aikatar masana’antu da kasuwanci da zuba jari tare da hadin gwiwar bankin masana’antu. An dai karkasu bashin ne zuwa kashi biyu, inda na farko za a bayar da na biliyan 2.5, sannan kashi na biyun ma zai kasance biliyan biyu wanda jamilla ya kama naira biliyan biyar.
Ministan hakar ma’adanai da bunkasa karafa, Olamilekan Adegbite shi ya bayyana hakan a wajen taron karawa juna sani wanda ya gudana a Abuja, domin mayar da hankalin yadda za a tallafa wa kananan kungiyar masu hakar ma’adanai. Haka kuma, Adegbite ya bayyana cewa, ma’aikatarsa ta yi wa sama da kananan kungiyoyi hakar ma’adanai rijista guda 1,495 tare da cibiyoyi masu sayan ma’adanan guda 368.
Ya ce, “a cikin kananan kugiyoyin hakar ma’adanai guda 1,495 da aka yi wa rijista, guda 140 ne kungiyoyin zinari. Yankin Arewa maso Yamma ne suka fi yawan kungiyoyin da aka yi wa rijista, yayin da Kodu masu Yamma ke da kaso dan kadan.”
Ministan ya kara da cewa, “a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2020, an sami yawan masu neman bashin hakar ma’adanai na naira biliyan 14.59 guda 138, inda ake ta kara amsar wasu daga baya.
Adegbite ya ci gaba da bayyana cewa, wannan rarraba kudaden ya yi karanci idan aka kwatanta shi da yawan mutanen da suke bukatar amsar kudaden, saboda sai masu nema sun cika wadansu sharudda na bankuna kafin a sami nasarar ba su kudaden. Ya kara da cewa, gwamnati tana aiki tukuru domin tabbatar da ganin cewa, an samu saurin rarraba kudaden.