Daga Sabo Ahmad
Sama da mutum ɗari ne, da ke da hannun jari a kamfanin mai na Oando suka miƙa takardar kokensu ga Majalisar tarayya, bisa ƙorafin da suke a kan hukumar gudanarwar kamfanin na ci musu mutunci da rashin iya mulki da kuma rashin ɗa’a wajen gudanar da harkokin kamfanonin mai.
An rubuta takardar koken zuwa ga shugaban kwamitin kula da manyan kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kuɗi na Majalisar tarayya, wadda ke ɗauke da sa hannun masu hannun jari guda 100, wadda ke nuna buƙatar rushe hukumar gudanarwar kamfanin.
Lokacin da yake miƙa takardar koken ga shugaban kwamitin na majalisar, Honarabul Tajudeen Yusuf, wanda mataimakinsa Honarabul Tony Nwuta,ya wakil ce shi, shugaban ƙungiyar masu hannun jarin, Ambasada Olufemi Timothy, ya koka kan gazawar humomi na kare muradun masu hannun jarin wanda ke zama babbar barazana wajen ci gaba gudanar da harkokin kasuwancinsu. Takardar wadda daga baya aka raba wa manema labarai , wadda ke nuni da irin matsanancin halin da kamfanin ya shiga tun kusan shekara uku da suka wuce. Takar ta ƙara da cewa, tun shekara ta 2013, rabon da a raba wa masu hannun jarin riba.
Ƙungiyar ta tabbatar da asarar sama da naira biliyan 159 a bayanan da ta rubuta na ƙarshen shekara ta 2016. Ganin irin ɗimbin asarar da aka a wannan kamfani, ya karya wa masu hannun jarin ƙarfin gwiwar cewa, da wuya a iya mayar da wannan asarar “Kyasa-kyasan da aka kai kotu na neman haƙƙi a hannun kamfanin sun kai na sama da naira biliyan 608 wanda ya wuce dukkan kadarar da kamfanin ya mallaka nesa ba kusa ba, wanda kuma samun nasarar masu neman haƙƙin babbar barazana ce ga ɗorewar kamfanin.
Haka kuma a takrdar koken an yi ƙorafin cewa, matakan da ka ɗauka ba su isa su warware matsalar bashin da kamfanin ya afka ciki ba.
“Rahoton Hukumar gudanar kamfanin na ƙarshen shekra ta 2016 ya nuna an yi asarar sama da naira biliyan 768; wadda kuma ta ta ƙarshen shekara ta 2015.
Saboda haka ganin irin waɗannan matsaloli ne suka sa, ya zama dole a miƙa koke ga hukumomin da abin ya shafa, domin su kawo ɗaukin yadda za a samu fita da cikin matsalolin.
A wata sabuwa kuma ƙungiyar masu hannun jari da ke sassan Arewacin ƙasar nan sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a Asokoro, inda suka buƙaci masu ruwa da tsaki a kan harkar mai da shigo don daidaita tsakanin masu hannun jari a kamfanin Oandon da Hukumar gudanarwar, don tseratar da kamfanin da barazanar da yake fuskanta ta durƙushe wa.
Da yake magana a madadin mutanensa, shugaban ƙungiyar amintattun masu hannun jari ta ƙasa, Alhaji Mukhtar Mukhtar, wanda kuma shi ne ya jagoranci zanga-zangar ya ce, rahoton da mai binciken kuɗin kamfanin Oando ya bayyan na shekara ta 2016 a shafi na 64 ya isa hukumar da abin ya shafa ta ɗauki mataki.