Masu Kiwon Kaji Sun Fitar Da Sabon Farashin Kaji Da Kwai

Jihar Ogun

Daga Abubakar Abba

Kungiyar masu kiwon Kaji ta kasa PAN reshen Jihar Ogun ta hada shawarwari a wuri daya domin fitar da sabon farashin kwai da naman  kajin da ake sayarwa a jihar.

A cewar kungiyar ta PAN, ta yi hakan ne domin masu sana’ar musanman ‘yan kungiyar su samu damar samun ribar da ta kamata kan jarinsu da suka zuba a cikin fannin na kiwon kaji a jihar.

Kungiyar ta ci  gaba da cewa, hakan ya zama wajbi, musamman idan aka yi la’akari da irin kokarin da kungiyar ke ci gaba da yi wajen samawar da masu sana’ar da kuma ‘ya’yanta mafita kan yadda za su ci gaba da samun riba mai yawa a fannin na kiwon kajin a jihar tare da samar masu da farashin da ya dace.

“Hakan ya zama wajibi, musamman idan aka yi la’akari da irin kokarin da kungiyar ke ci gaba da yi wajen samarwa da masu sana’ar da kuma ‘ya’yanta mafita kan yadda za su ci gaba da samun riba mai yawa a fannin na kiwon kaji a jihar tare da kuma samar musu da farashin da ya dace.”

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar  mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Yunin shekarrar 2021 ta kuma samu sa hannun Sakatare Janar na kungiyar, ta bayyana cewa biyo bayan fashin baki da aka yi kan yadda abincin da ake ciyar da Kajin musaman masara da sauran kayan kiwon a jihar.

Bugu da kari, shawarwarin da kungiyar ta bai wa ‘ya’yanta  sun hada da, sayar da kwan kaji samfurin Jumbo  kan Naira  1,600 na ko wane kiret daya.

Har ila yau, manyan kwan kajin za a sayar kan Naira 1,500  zuwa sama, sai kuma wanda za a sayar kan Naira 1,400 zuwa 1,500 da wanda za a sayar kan Naira 1,300,  sai kuma kwan da za a sayar kan Naira 1,200.

Bugu da karin, naman Kaji na   za a sayar kan naira 900 zuwa naira 1,000 na ko wanne kilogiram daya da kuma wanda za a sayar kan kilo daya  daga naira 1,450 zuwa naira 1,550.

Har ila yau kuma, kungiyar ta bayar da shawawa kan su gagauta yin amfani da sabon tsarin farashin.

Exit mobile version