Connect with us

LABARAI

Masu Korona A Nijeriya Sun Karu Zuwa 1,337

Published

on

A Nijeriya ana ci gaba da samun masu cutar Korona, inda Cibiyar dake lura da dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC suka wallafa a shafinsu cewa an kara samun adadin mutum 64 da suke dauke da Korona a sassan Nijeriya bayan sakamakon gwajinsu ya fito.

NCDC sun wallafa hakan ne a shafinsu na Twitter a daren jiya Talata.

Wuraren da aka samu masu Korona din sun hada da;

34 a Legas
15 a FCT
11 a Borno
2 a Taraba
2 a Gombe

Ya zuwa karfe 11:20 na daren 27 ga watan Afrilun 2020, Nijeriya na da mutum 1337 da suke dauke da Korona.

A yayin da aka sallami 255, inda kuma 40 suka riga mu gidan gaskiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: