Masu Koyarwa ‘Yan Kasar Jamus Da Suka Lashe Kofin Zakarun Turai

Daga Abba Ibrahim Wada

Masu koyarwa ‘yan asalin kasar Jamus guda uku ne da suka lashe gasar cin kofin zakaru na Champions League a jere a shekarun nan, kuma wadanda suka yi aikin koci a gasar Bundesliga.

Jumulla masu horar da kwallon ‘yan kasar Jamus biyar ne suka yi wannan bajintar da kuma lashe Champions League bakwai tsakaninsu wanda hakan za’a iya cew wani ci gaba kwallon kafa ta samu musamman a Jamus.

Wanda ya daga kofin bana shi ne tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Mainz da Borussia Dortmund, Tuchel, wanda ya ja ragamar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta doke Manchester City 1-0 ranar Asabar din ta gabata.

Tuchel ya bi sahun mai koyarwa Jurgen Klopp wanda ya dauka a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da kuma Hansi Flick wanda ya lashe kofin na Champions League a kungiyar Bayern Munich.

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Mainz da Dortmund, Klopp ya jagoranci Liverpool ta yi nasara lashe kofin a kakar wasa ta 2018 zuwa19, shi kuwa Flick ya yi bajinta a Bayern Munich, inda kungiyar ta lashe kofi shida a shekarar 2019 zuwa 2020.

Hakan na nufin koci biyar daga Jamus ne suka ci Champions League, tun bayan da aka sauya fasalin gasar a shekarar 1992 daga European Cup kuma sauran biyun sun hada da Jupp Heynckes a shekarar 1997 zuwa 1998 a Real Madrid da kuma 2012 zuwa 2013 a Bayern Munchen da kuma Ottmar Hitzfeld a shekarar 1996 zuwa 1997 a Dortmund da kuma shekarar  2000 zuwa 2001 a Bayern Munich.

Jupp Heynckes da kuma Ottmar Hitzfeld sune kadai suka lashe Champions League ‘yan kasar Jamus kuma sau bibiyu sai dai tsakanin Klopp da Tuchel tsoffin kocin Mainz da Dortmund sun kai wasan karshe karo hudu a Champions League a tsakaninsu.

Kuma kowanne daga cikinsu an buge shi a kai wa karawar karshe a kakar kwallon kafa  da wata ta zagayo sai ya kara kwazo ya kuma lashe Champions League bugu da kari Klopp wanda ya buga wa Mainz wasanni 340 a matakin dan wasa ya kai kungiyar Bundesliga a karon farko da ya karbi aiki a shekarar 2003 zuwa 2004.

Bayan kakar wasa  bakwai a Mainz daga nan ne Kloop ya koma Dortmund da horar da kwallon kafa a shekarar 2008 sannan a kungiyar da ya ci Bundesliga biyu a jere a kakar wasa ta 2010 zuwa 2011 da kuma 2011 zuwa 2012 da karin cin wasu kofunan gasar Jamus a kungiyar.

Daga nan ne Dortmund ta wakilci Jamus a kofin zakarun turai na Champions League a shekarar 2013, inda karawar karshe ta kasance tsakanin kungiyoyin Bundesliga, inda Heynckes na Bayern ya lashe sai dai daga nan ne Kloop ya yi jira har kakar wasa shida, kafin daga baya ya lashe gasar ta Zakarun Turai.

Tuchel ya bi sawun matakin da Klopp ya yi na jan ragamar Mainz da Dortmund, wanda ya kai Mainz gasar Zakarun Turai a karon farko a tarihin kungiyar, sannan ya lashe DFB a Dortmund a shekaarar 2017.

Kuma Flick ne ya hana Tuchel cin kofin Champions League a shekarar 2020, bayan da Paris St Germain ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da ci 1-0 kuma Bayan da Tuchel ya yi rashin nasara a hannun Flick a shekarar 2019 zuwa 2020, daga nan ne kocin ya kara kwazo ya kuma lashe Champions League a Chelsea kuma a karon farko a shekarar 2020 zuwa 2021.

Flick ya yi bajintar cin kofi shida a kakar farko da ya ja ragamar Bayern Munich ciki har da DFB Cup da Champions League da FIFA Club World Cup da German Cup da kuma European Super cups.

Flick ya kuma kara cin kofin Bundesliga a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 ya kuma ajiye aiki da cewar zai maye gurbin Joachim Low da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana a matsayin kociyan tawagar kasar Jamus.

Tun a bara ya kamata a bugu gasar cin kohin nahiyar Turai, amma cutar korona ta kai tsaikon da aka daga wasannin zuwa 2021 sai dai a yanzu za’a fara buga gasar ne a ranar 11 ga wannan watan.

Exit mobile version