Za mu so ka fada wa masu karatu sunanka
Sunana Is’haka Usama
Daga wace Jiha kake?
Katsina KT Wanti Dutsimma
Wace irin sana’a kake yi?
Sana’ata ni dai wanzami ne kuma bayar da maganin gargajiya a na Utako Bilage, kusa da Ofishin NEPA.
Kana bayar da maganin gargajiya, kamar wanne da wanne?
A gaskiya domin Allah a nan ina da magunguna da yawa , da fari dai mai cutar shanyewar barin jiki a kalla in Allah ya sa ya kirawo ni game da aikin sati guda an warke. Abin da ya danganci kuma bu su ko binni da aka yi wa mutum asiri haka, in sha Allahu in ka kirawo ni idan na zo ina ganin hayaki a cikin gidan, ya yin da kuma ake ganin a kasuwa an yi maka binni ne, wannan ma ana kira na ina tonewa, yayin da kuma aka ce a sana’ar ce an yi maka sammu, ko makaru, ko jifa, ko kuskurar baki, ko kambun baka, ana zuwa a dauke ni na je ka karya. Na je har Kano, zuwa su kauyen mama wajen Jos, su Akwanga duk ana zuwa a dauke ni game da irin wadannan ayyukan.
Sannan ina da magungunan su Hakiya, Tsawarya, wanda a cikin sakan 10 na cire su da yardar Allah. Mutumin sa ba ya gani saboda tsawarya ta fito masa ko hakiya ko yanar ido, idan ya zo gabana cikin yardar Allah ko sanda yake yawo da ita cikin sakan 10 zai yar da ita. Mai anfani da tabarau ma, in da yana sawa ne da sunan ba ya gani har an je an auna masa ido, in sha Allahu in dai aka zo gabana na yi wannan aikin cikin sakan 10 ba zafi ba komai kamar cirar kaya ne, addu’o’i ne da kuma magunguna irin namu na Hausa nan ma cikin dan kankanin lokaci an wuce wajen.
A bangaren cutar shanyewar barin jiki kuwa, wato (Paralyze) wani lokacin aljanu ake turowa mutum, sammu ne wani kuma tarar da su ake yi, mutum ya je ya tako aljani, to game da irin wannan aikin kira na ake yin a zo na yi maganin abin.
Banagaren kuma da ya shafi mayu, in an ce ga wane maye ya kama shi, wannan ba sai an je ko ina ba, take yanke wannan raba gardama nake sunan mayen ne zai fada cewa ni ne wane ni na kama shi lokaci kaza, wannan aiki na ne ko a yau ko gobe idan an kira ni zan yi, kuma kai da wannan maye har abada.
In an so na makanta maye zan makanta shi, in an so kuma na lalata rayuwarsa gaba daya sai ya gani zai ci, wannan ma zan iya, in sha Allahu ta wannan bangaren a kwai magunguna da dama a nan da ba su ma iya lissafuwa. Idan kuma mutum ya zo larurarsa sai mu duba maganin in akwai mu ba shi, idan babu mu ce babu. Gaskiya mu ba irin wadanda suke yawo ba ne, muna zaune wuri guda ne, domin magani na gaskiya shi ke sayar da kansa, in za ka shekara dubu kana wucewa ta wurin da nake za ka ganni, kuma ba na tara jama’a da sunan ina wasa da kaza, kai za ka zo ka karbi magani, don magani na gaskiya shi ke tallan kansa baki ba ya sayar da magani.
In ka ji mutum yana cewa nid an sarki ka za ne ko dan sarki ka za, karshenta da z aka je kauyensu sai ka samu ko kanwa ba a sayarwa a gidansu, amma da ya zo nan Abuja kuma shi ne sarkin masu magani.
Ba na baro Katsina sai na bar wakilaina ko da za a kawo mara lafiya ko kuma in za a nemi mu je wani wuri. Sannan na kan bar wakilina a nan idan zan je gida, kuma wani abin ina aiwatar da shi ko da ban a Katsina. Ina daga nan zan yi aiki, kawai cewa zan yi a ba ni cikakken sunan mutum ko daga ina nake zan yi masa aiki. Misalin irin su karaya da sauransu ko ba na kusa zan yi wa mutum aiki kuma in sha Allahu a dace.
To ita wannan sana’a gadonta ka yi ne ko kuwa dai taka haye ne.
Wannan sana’a gadon ta na yi gaba da baya, domin mahaifiyata wanzamiya ce, mahaifina wanzami ne, kakana wanzami ne, don yanzu haka wanda yake sarkin aska na yanzu a cikin gidanmu yayana ne, daga shi sai ni domin a yanzu idan aka ce zai yi murabus ko wani dalili to ni za a nata.
Da yawa za ka ga masu sayar da magani za a zo ana neman maganin maleriya ko na Taiftot, su kuma maganin karfin maza da su, amma don cin amana haka za su dauki magani karfin mazan nan za su bayar a matsayin maganin Maleriyar nan su je su yi ta sha, kuma suka ba da maganin nan ba za ka sake ganinsu ba har abada ba zaka kara ganinsa ko mai kamanninsa ba.
To irin wadannan mutane su suke bata mana suna, shi ya sa za ka ga da mutum ya ji bai da lafiya, da cutar da ta dace a je asibiti da wadda ba ta dace ba duk sai ka ga ana tafiya asibiti, domin wasu na bayar da maganin da ban a cutar da ta kama mutum ba, suna lalata mana suna. Idan ka tara masu sayar da magani mutum 100 da wuya ka fitar da mutum 10 wadanda suke shiga jeji su debo magani, sais u je wurin ‘yar mai ganye su auno su rika sayarwa mutane.
Ka kai kamar shekara nawa kana aiwatar da wannan sana’a?
To a gaskiya tun daga tasowata ina dan karami mahaifina ya ke shiga daji da ni yake nuna min itatuwa, wannan maganin kaza ne wannan na kaza ne in ka hada shi da kaza zai zama maganin kaza, a haka na taso.
Wane irin ci gaba ka samu a wannan sana’a taka?
To tsakanina da Allah na samu ci gaba da dama, domin a yanzu haka da ita na yi aure, na sayi gona kuma na sayi fili na yi gini, ka ga ai ta gama yi maka komai. Kuma duk sanaar da za a ce idan ka tashi zaka je ka yi kuma ka ci ka sha a cikinta ai an samu arziki, babu abin da zan ce sai dai ina yi wa Allah godiya.
To wace irin matsala kake fuskanta a hukumance?
Gaskiya daga kan soja, dan sanda, zuwa kan ko wane jami’in tsaro, tsakanina da Allah ban taba samun matsala da kowa ba, domin kuwa na farko ba na raina kowa, duk yadda ka dara ni ko da dakika daya ne zan girmama ka, don haka nib a ni da wata matsala da kowa.
A karshe wane kira z aka yi gay an uwanka masu irin wannan sana’a?
Ina kira gare su da su kiyaye abubuwa guda biyar su ne; gaskiya, amana, tsoron Allah su kuma kaucewa ha’inci, shi ne idan ba ka da magani kawai ka ce babu kawai, domin idan fa ba ka ganin Allah shi fa yana ganinka