Connect with us

SIYASA

Masu Munanan Maganganu Kan Shugaba Buhari, Daukar Nauyinsu A Ke Yi –Dakta Abdul’azeez

Published

on

Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, DAKTA BATURE ABDUL’AZIZ ya yi shelar cewa wadanda suke munanan kalamai akan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari daukar nauyinsu ake yi. Shugaban ya yi wadannan bayanan ne a makon da ya gabata yayin zantawarsa da wakilinmu a Kano.

Ko me Dakta zai ce game da abin da ke faruwa na suka da wannan gwamnati ke fuskanta a ‘yan kwanakin nan?

Wato abin da ke faruwa game da abin da yake faruwa dangane da miyagun ‘yan jaridu wadanda suke mummunar fassara akan Shugaban Nijeriya, irin wadannan ‘yan jaridu in ka lura da tsarin aikinsu wato kamar ma sanya su a ke yi su yi maganganu kawai, don su dagula kasa su hargitsa kasa, damin suna iya amfani da kalmomi na kabilanci da na addini da kuma na bangarenci.

Ko akwai misalai na dalilin da ya sa ka ke wannan zargi?

eh, wato akwai wata jarida kwanaki da ta yi bayani kwanaki cewa, wai ya koma bayan Fulani. Idan ba abu irin na miyagun ‘yan jaridu da muke da su ba, shi dai Buhari bafulatani ne, komai abinka duk yadda ka kai kawo babu yadda za a yi y ace shi ba bafulatani ba ne, na biyu kuma dan Nijeriya ne. Yadda yake dan Nijeriyar nan Allah ya waddara shi dan kabilar ne, to ai ba dama ya ce shi ba dan kabilar ba ne, to kuma kawai don yana bafulatani shikenan sai ka ce abin da Fulani suke yi da ruwansa ko da saninsa, ko da yardarsa? Me ya hada shi da su, kuma ta ina ya hadu da su, wace hujjar ce ta cewar yana tare da masu yin wannan abu?

Fulanin nan in da yana tare da su, to da ba za ayi ta kshe su ana ta sace musu shanu bai yi wani abu a kai ba. Amma ka gat un da aka fara rigingimun nan, misali ka dauki na jihar Filato, ai wadanda aka kashe a rigingimun kusan kashi 65 zuwa 70 duk  Fulani.

Dauki rikicin jihar Taraba, fiye da kashi 80 cikin dari duk Fulani aka kashe, sannan ka dauki rikicin jihar Beniwe, kusan kashi 75 Fulanin aka kashe. Kuma da na taraba, da na Jos, da ainihin na Beniwe, to wadannan jihohin gaba daya ba ma fulanin aka kashe kadai ba dukiyarsu da aka sace, kusan saniya 35,000 suka bata a wannan hayaniya. Kuma an kona masu gidaje da dama, an kona kauyka sun 60, kuma dabbobin na ba wai kama su ake yi a matsayni sat aba, wato kashe wadansu ake yi, wadansu kuma a kashe su. A takaice irin asarar da bangaren Fulani suka yi, sun asara ta sama da kashi 90 cikin dari na dukiyarsu, kuma wadanda kake cewa su kake so ko kashiii 15 cikin 100 na dukiyarsu ba su yi asara ba.

To amma don jaridu ne naku na kabilanci, jaridun naku masu haddasa fitina, jaridun naku da ba sa fadar alheri, duk sanda magana ta taso sai ku fade ta yadda kuke so, ko da yake ban ce duk ‘yan jarida ne suke da wannan ra’ayin ba, wasu ne daga cikinsu, su kamar dan dauke su kwangila ne, su fadi maganar da suka ga dama, wadda za ta kawo rikicin addini, rikicin kabilanci, rikicin bangarenci, da bata wa mutum suna na siyasa, su ce ai ane da wane ya fito daga bangare kaza.

Wanne kira ka ke da shi ga irin wadannan mutane?

To ina kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jaridu irin wadannan a gane su, domin kashi 5 cikin kashi 10 na ‘yan jaridu su ne fitilar duniya, kuma su ne fitilar Nijeriya, su suke sanar da duniya yadda ta kwana da yadda ta tashi. Su suke sanar da Nijeirya ya ta kwana da yadda ta tashi, ba shakka sun cancanci yabo.

Amma wadancan bata gari, wadanda ba ‘yan kishin kasa ba ne. ai ka fito fili ma ka ce Shugaban kasa ya koma bayan wata kabila, to ko dai wannan dan jarida a buge yake bai san abin da yake ba, ko kuma a a abin da iyayen gidansa suke ganin za su yi furofaganda da shi, ta hanyar da suk ganin za su iya kada Buhari ranar zabe, amma ba su samu hanya ba, sai ta furofagandar karya da son zuciya. Saboda haka ‘yan Nijeriya na sha gaya muku a cikin irin wannan hira cewa, shakka babu akwai bara gurbi a cikin ‘yan jaridu, kuma su ma ‘yan jaridun sun san da haka. Allah ya tsare mu da su Allah ya mayar da aniyarsu kansu wadda ba ta alheri ba.

Sau da yawa idan ka ji rikici ya tashi akan kabilanci, to wadannnan ‘yaridu su suka haddasa don su tashi hankalin jama’a. to wannan abin da ba su sani ba shi ne, zakaran da Allah ya nufa da cara ana muzuru ana shaho sai yayi. Wannan Shugaban kasa namu mai ci wato Muhammadu Buhari, Shugaba ne wanda ‘yan Nijeriya suka shaide shi da ma kasashen waje. Saboda duk irin cigaban da kasashen waje suka samu, san samu ne saboda tsayawa kan gaskiya da kuma aiki da gaskiyar, da kuma ba wa ko wane dan kasa hakkinsa, kuma duk wanda ya ci hakkin ‘yan kasa a tuhume shi a gurfanar da shi gaban kotu a hukunta shi.

Domin irin mutanen da suke sace dukiyar kasar su ne ke biyan wadannan ‘yan jaridu bata gari kudi mai yawa don su kao hargitsi da hautsini a Nijeriya, kuma wannan manufa ta su bata yi nasara ba, kuma ba za tayi nasara ba. Domin in lura za ka ga kullum Buhari cigaba yake, kuma kasar ma kara cigaba take yi. Saboda kullum ayyuka ake yi, kuma ba fada ake yi da baki ba, to kai mai soke-soke baka san shure-shure baya hana mutuwa ba?

Kuma ya kamata ka fahimta cewa, iyayen gidan naka da kake takama da su wadanda ake ganin idan an taba su kamar duniya za ta ruguje su ake bi ana kamawa? To yanzu fa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa su a gaba a takaice su ake tabawa, duk wanda ya taka doka, ko ya ci amanar kasa in sha Allahu Buhari zai ga bayansa. Kuma su wadannan ‘yan cin amanar kasa wanda suka hada wata kungiya da Shugabansu wani dattijo da ya zama kamar shi ne Shugaban MAFIYA a takaice duk wanda y ace ba zai yi da shi ba sai ya ga bayansa, to tsoho karya ne, sai dai Buhari ya ga bayanka a siyasance, kuma ko yanzu ya karya maka alalar siyasa, domin duk wani siddabaru ko dabo da kake zaton siddabarun nan ko dabon nan bai tasiri akan Buhari ba, bai aiki ba kuma ba zai aiki ba.

Saboda haka ‘yan Nijeriya a kula da kyau, Nijeriya kasarmu ce mu ne za mu ciyar da kasarmu gaba, kuma mu za mu kawo zaman lafiya a kasarmu, don haka mu guji  yada jita-jitar karya, mu kauce wa yada matsalolin addini. Musulmi yayi addininsa, shi ma Kirista ya yi nasa addinin, haka Allah yaso ya hallici kowa da Musulmin da wand aba Musulmi ba, haka harshe kowa da irin yadda Allah ya so ya yi shi. Allah yana fada Alkur’ani cewa, shi ne ya halicce ku kuma ya sanya ku kabila daban-daban don ku fahimcin hakan, amma kuma mafi girma a wurin Allah wanda ya fi ku tsoron Allah.

A wani kaulin Allah y ace, in da ya so sai ya halicce ku iri daya, addini daya harshe daya. Amma da ya so sai ya banbanta ko wane yare, ka ga ke nan ko wane yare da kan shi daga Allah yake, baka da ikon kushe shi ko raina shi. Saboda dukkan mu Allah ne ya halicce mu, saboda haka idan an kula bangaren Arewa da bangaren Kudu maso Yamma, duk bangarori ne da haka Allah ya so su zauna hakan, amma ko wane zaman kansa yake, kuma daga baya aka zo aka hada su wuri daya, yau shekara 58, da wannan haduwa, saboda haka a 58 din nan ko wane bangare ya yana da babbar gudunmawa ajen gina Nijeriya, kuma babu wata matsala don ka hada bangare ukun nan ka tashi Nieriya ta zama kasa daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: