Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Samar Da Karin Jami’o’i

bySani Anwar and Sulaiman
7 months ago
Gwamnatin tarayya

Ci gaba da mayar da manyan makarantun jihohi zuwa jami’o’in gwamnatin tarayya tare da sake kafa wasu sabbi da gwamnatin tarayya ke yi, na ci gaba da shan suka a wajen wasu masu ruwa da tsaki.

Adadin jami’o’in gwamnatin tarayya a wannan kasa, ya haura 63.

  • Sin Ta Mika Tallafin Wasu Jirage Marasa Matuka Na Inganta Noma Ga Kasar Zambia
  • Azumi Ya Dara Wa Sauran Ibadu

Yayin da ake kokarin daukar matakan magance yawan wadannan manyan makarantu da kuma fadada hanyoyin samun ilimi, masu suka sun yi gargadin cewa; hakan zai iya haifar da asarar samun ingantaccen ilimi.

Masu ruwa da tsakin sun jaddada cewa, idan ba a yi kokarin magance wannan matsala ba, hakan na iya kawo koma baya a fannin na ilimi, sannan kuma; ci gaba da kirkirar sabbin jami’o’in gwamnatin tarayya, na iya haifar da kara tabarbarewar harkokin ilimin a fadin wannan kasa baki-daya.

Har ila yau, masu ruwa da tsakin, sun bayyana damuwarsu kan cewa; kyautuwa ya yi a ce jami’o’in da ake da su, sun mayar da hankali wajen inganta ayyukan koyarwarsu da bincike da kuma samar da kayan ayyukan koyarwa.

Sun kuma bayyana cewa, wajibi ne gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta manyan makarantun da ake da su na tarayya da kuma jihohi, ta hanyar samar da wadatattun kudade, inganta abubuwan more rayuwa da kuma tabbatar da ganin ma’aikatan jami’i’on, sun samu horo na musamman da suke bukata da kuma tallafa musu.

Wani mai ba da shawara a kan harkokin binciken ilimi a Jami’ar Abuja, Humphrey Ukeaja, ya gano wasu damammaki da kalubale iri-iri da aka samu kwanan nan.

Masanin ya yi nuni da cewa, rashin samun wadatattun kudade a fannin ilimi a Nijeriya, ya zama wani babban al’amari. “Idan kuna son yin wannan sauyi misali, mayar da jami’i’o’i zuwa na gwamnatin tarayya, har yanzu a kwai ayar tambaya, shin za ku inganta su ne kokuwa inganta kudaden da za a bai wa sabbin jami’o’in? Domin kuwa, wannan ba karamin kalubale ba ne. saboda haka, gwamnati tana da kyakkyawan kudiri ne na daukar cikakken nauyin wannan ilimi?”.

Canzawa tare da kara wasu makarantu ba tare da daukar cikakken nauyinsu ba, zai sa ba za su iya tsayawa da kafafunsa, wanda a karshe ko kadan ba za a samu abin da ake nema ba na biyan bukata, in ji shi.

Farfesa Ukeaja, na da ra’ayin cewa, kafa jami’o’in tarayya a wurare kamar Kachia, zai taimaka wajen inganta ilimi tare da rage tazarar da ke tsakanin birane da kauyuka ta fannin samar da ilimi. “Don haka, idan har za a samar da jami’o’i a wuraren da suka dace, babu shakka wannan zai zama wani babban ci gaba”, in ji shi.

Ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta kara yawan kudade ga fannin ilimi tare da fadada hadin gwiwa da jami’o’i masu zaman kansu, domin inganta jami’o’in, bai wa malamai horo na musamman da sauran makamantansu.
Har ila yau, kungiyar daliban Nijeriya; sun yaba da matakin, amma kuma sun nuna damuwa a kan lamarin.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar dalibai ta kasa (NANS), Kwamared Samson Ajasa Adeyemi, ya bayyana jin dadinsa kan kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalolin ilimi a Nijeriya, musamman kan yadda take mayar da makarantun jihohi zuwa na tarayya.

Sai dai ya koka da cewa, daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar fannin na ilimi a Nijeriya, ya hada da rashin isasssun kudade.

Ajasa ya yi nuni da cewa, da dama daga cikin wadannan manyan makarantun gwamnati, sun dogara ne da kudaden basussuka wajen tafiyar da makarantun, sannan akwai bukatar aiwatar da gaskiya wajen aiwatar da kasafin kudin yadda ya kamata, domin tabbatar da ganin an yi amfani da wadannan kudade yadda ya dace.

A nasa bangaren, wani dan kishin kasa, Mista Tochukwu Osuagwu, ya bukaci gwamnati ta kara zuba hannun jari a jami’o’in da ake da su, domin inganta su yadda ya kamata.

“Me zai hana a mayar da hankali wajen inganta jami’o’in da ake da su a fadin wannan kasa baki-daya, ko shakka babu, Nijeriya za ta ci gaba idan muka riki junanmu da gaskiya.

“A bayyane yake cewa, jami’o’inmu na cikin wani mummunan yanayi, wanda ba haka ya kamata al’amarin ya kasance ba, kyautuwa ya yi a ce jami’o’inmu sun samu wadatattun kayan aiki da ci gaba kamar yadda ake gani a wasu sauran kasashe”, in ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Labarai

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Next Post
Sin Ta Yi Maraba Da Ziyarar Dan Majalisar Dattawan Amurka

Sin Ta Yi Maraba Da Ziyarar Dan Majalisar Dattawan Amurka

LABARAI MASU NASABA

A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version