Connect with us

TATTAUNAWA

Masu Sana’ar Fitar Da Amfanin Gona Waje Ba Ma Samun Tallafin Gwamnati – Alhaji Tanimu 

Published

on

Shi ne shugaban kamfanin (ATH Agro global concept). Matashin dan kasuwa, kuma dillalin fitar da kayan amfanin gona zuwa kasashen waje, ya nuna irin rashin jin dadinsa ga rashin tallafin gwamnatin tarayya a gare su, Alhaji Tanimu ya bayyana haka cikin tattaunawarsu da wakilinmu akan haka da kuma wasu batutuwa, kamar dai za ku karanta kamar haka:

 

Masu karatu za su sanin tarihin rayuwarka a takaice

To ni sunana Alhaji Tanimu Hamza Dakata, An haife ni a Jihar Kano a dakata, a nan girma kuma a nan na yi karatun firamare na a (Kawaji jigirya special primary school)daga 1991 zuwa 1997. Daga nan kuma sai na samu damar shiga makarantar (Gobernment secondary commercial). A shekarar 1997 zuwa 2003, bayan na kammala sai na tafi makarantar share fagen shiga jami’a wato (Cas) inda na yi zana jarrabawar(IJMB). Na yi shekara biyu daga nan kuma sai na tafi kwalejin ( Aminu kano college of legal and islamic) na karanta hausa and language. Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata.

 

Aksarin ‘yan kasuwa sun gaji kasuwanci ne a wurin mahaifansu, shin kai ma ka gada ne ko yaya abin yake?

Wannan gaskiya ne don mu wannan kasuwanci mun gaje shi ne daga wurin mahaifanmu, shi ne sana’ar da duk Kano idan ka ce dakata bawan da bai santa ba akan wannan sana’ar ta karo da sobo ba, wannan shi ne.

 

Daga wacce shekarar aka fara wannan sana’ar ne?

A gaskiya mu dai mun taso a gidan mu mun ga ana wannan sana’ar daga baya kuma aka farayin ta a kamfanoni wanda yake a nan  ‘Independence road’ dake Bompai inda yanzu aka fadada harkar ana yin ta sosai a cikin Kano da sauran jihohin Arewa. Gaskiyar lamari tun ina dan shekara bakwai (7), Ana yi a haka har aka zo yanzu wanda akalla na kai kusan shekara 37 a cikin wannan harka.

 

Masu karatunmu zasuso karin haske agame da shi sobon nan kune kuke nomawa koya abun yake?

Shi wannan sobon da kake gani ba mu ne muke nomawa ba mu dai kawai muna bin kasuwannin kauye muna sayowa muna kawowa kamfani muna ba wa mata suna gyarawa, sai a fita da shi a cikin mota zuwa legas su kuma su tura da shi zuwa kasashen waje amma a nan gida Nijeria ake sarrafa shi.

Idan ka kira mu da dillalai baka yi laifi ba, shi sobon nan ana kai shi Kasar Medico, a shekarun baya medico ita ce kasa mafi girma a wajen amsar sobo a duniya, daga ita sai Kasar Amurka, sai China duk da dai ita Kasar China bata fi shekara uku 3 da fara karbar sobon ba amma dai Medico ita ce kasa mafi karbar sobo a duniya.

 

A kalla mutane nawa ne daga maza zuwa mata suke aiki a wannan kamfani, don na ga da mutane?

To gaskiya dai yanzu wannan aikin daga maza gami da mata a kalla akwai mutum sama da 300, wadanda suke aiki suna samun na abinci, kuma mafiyawancinsu,sun dogara da Allah sun dogara da wannan aikin tunda wasu da yawa sai sun yi wannan aikin idan an biyasu sannan su say wa ya’yansu abinci. Alhamdulillah kusan kullum muke biyan matanen kudin aiki duk wanda ta yi mana aiki ranar za mu biya ta ba wai sai gobe ko jibi ba, sannan bangaren maza da yake mu aikinmu ya fi karkata ga bangaren mata saboda mata sune suke zama su dukufa su ne suke yin aikin, za ka ga mazan ba su fi mutum 50 ko 40 ba,amma matan sun fi yawa gaskiyar lamari.

 

Gwamnatin tarayya tana mayar da hankali wajen ba da rance ko irin wannan tallafi na kudade ko rance ya iso gare ku?

A gaskiyar lamari muna da korafi akan wannan, dalili kuwa shi ne gwamnatin tarayya bata bamu wani tallafi domn sun fi mai da hankali kan masu harkar shinkafa, kuma kaga dukkan haraji muna biya, kama daga matakin gwamnatin tarayya, jihohi, haka ma matakin kananan hukumomi muna biyan harajinmu. To amma wannan magana ta gaskiya ba ma samun komai daga cikin tallafin gwamnati, ka ga kamar shi sobo shekaru uku 3 da suka wuce mun samu matsala babu wani hobasa da gwamnatin tarayya ta yi mana domin mun sami matsala a Medico mun yi ta kokari a je a dawo, wanda har wakilai muka tura zuwa Medico suka je suka zauna da gwamnatin kasar, sukace sai gwamnatin tarayya ta sanya baki sannan za ta cigaba da karbar wannan sobon, amman har yanzu ba’a samu shawo kan matsalar ba.

Muna kira ga gwamnatin tarayya data taimaka ta shigo cikin wannan sana’ar tamu, duba da irin mutanen da suke samun aikin yi ba tare da suna jiran sai gwamnati ta ba su aikin yi ba. Sannan da ta shigo cikin lamarimmu da Kasar medico ta ceto mu, mu ‘yan Arewa tun da wannan sobon da kake ganinsa a Arewacin kasar nan ake samu,ba’a samu a kudancin Nigeria, musamman bangaren Katsina, Kano, Bauchi, Jigawa, Zamfara da sauransu, don haka muna sanar da gwamnatin tarayya cewa, sobon nan a kalla, ana fitar da sama da tan 500,000 a duk shekara don Allah a taimakama na, a ceto mu daga cikin wannan halin da muke ciki don Allah.

 

Menene sakonka na karshe?

Sakona na karshe shi ne, don Allah gwamnatin tarayya ta shigo cikin wannan lamari musamman a kara tsabtace mana wannan harka babu wata harka da muka iya in ba wannan ba, musamman ka ga ita harkar karo ta lalace, haka citta, a taimaka mana saboda yara da suke tasowa a taimaki ‘yan Arewa shi ne sakona na karshe Allah ya bamu sa’a amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: