Masu Sana’ar Shayi Sun Koka Da Tsadar Burodi

 

Daga Abubakar Abba

Wasu masu sayar da shayi a jihar Kaduna sun koka matuƙa game da tsadar burodi, wanda shi ne abokin tafiyar shayi, duk da faɗuwar farashin kayayyakin da ake buƙata wajen sarrafa shi.

Masu shayin waɗanda suka ce tun da yanzu kayan sarrafa burodi kamar fulawa, da yis da sauransu sun sauka, kamata ya yi masu gidajen burodi su rage farashinsa.

Haruna Suleiman wanda aka fi sani da Maikuɗi mai shayi, shi ne sakatare na ƙungiyar masu shayi a jihar Kaduna, ya shaida wa BBC Hausa cewa, tun da farashin kayan hada burodi sun yi sauƙi, to ya kamata ƙungiyar masu yin burodi a ko’ina cikin Nijeriya ta yi la’akari da halin da ake ciki a ƙasar musammam ma dai talakawa, a rage farashin burodi.

Maikuɗi mai shayi, ya zargi masu gidajen burodi da cewa da za a ƙara samun hauhawar farashin fulawa bayan saukowarta a baya-bayan nan, to da sun kuma tsawwala kuɗin burodin, duk da yake sun ƙi saukar da farashinsa a yanzu.

To sai dai, shugaban gidan burodi na Tahir Bakery a jihar Kaduna, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar masu burodi a Arewacin Nijeriya, Alhaji Bashir Tahir, ya ce an samu matsala kwanakin baya a lokacin da gadar Jaba wadda ake bi wajen zuwa Arewacin ƙasar daga Kudu, ta karye inda hakan ya janyo kayayyakin haɗin burodin suka yi ƙaranci a kasuwa.

Alhaji Bashir, ya ce sakamakon ƙarancin kayayyakin, sai farashin kayan haɗin burodin ya tashi, to amma an gyara gadar yanzu kaya sun wadata a kasuwa sai dai duk da haka farashin kayan bai koma kamar a baya ba.

Don haka ya ce, yadda ake tunanin kayan sarrafa burodi sun sauka, gaskiya ba su sauka ba.

A kwanan baya dai tsadar burodi ta tilastawa wasu masu cinsa dainawa musamman masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Exit mobile version