Connect with us

LABARAI

Masu Satar Mutane Sun Halaka Babban Dan Kasuwa Da Sace Wasu A Lokoja

Published

on

Wani shahararren dan kasuwa da ke jihar Kogi mai katafaren shagunan da ake kira Chucks Supermarkets a birnin Lokoja, Mista Nicholas Ofodile da kuma wasu mutanen sun rasa rayukansu a wani hari da ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka kai musu a kauyen Gegu Beki da ke kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja, a ranar larabar nan.
Wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 6.30 na sanyin safiya a yayin da masu garkuwa da jama’ar suka kai wa wata babban mota kirar Ludury Bus mai rubutun CEN Nigeria Limited a jikinta, wanda aka cire lambarta da kuma sauran motocin da suke balaguro a kan babban hanyar Lokoja zuwa Abuja hari, a Gegu Beki da ke yankin karamar hukumar Kogi ,inda suka hallaka mutane da dama, sannan suka yi garkuwa da sauran mutanen da ba a san adadinsu ba.
Wani ganau da ya shaida lamarin, ya ce masu garkuwa da mutanen wadanda yawansu sun kai 15 sun datse babbar hanyar a yayin da suka hango motocin na dannowa a guje, inda ya kara da cewa wasu motocin sun rikice inda suka kauce kan hanya. A cewarsa, ganin haka, nan da nan ‘yan bindigan suka bude wa mutanen da ke cikin motocin wuta kuma nan ta ke suka hallaka mutane da dama, a yayin da suka yi garkuwa da yawancin mutanen dake cikin motar bas din kirar ludury.
A bangare guda kuma, kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), reshen jihar Kogi, Mista Emmanuel Abe wanda shi ma ya tabbatar da aukwar lamarin, ya ce jami’ansa sun kansance a wajen da lamarin ya faru don kwashe wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti tare da kwashe gawarwakin mutanen da suka mutu a sakamakon harin.
Haka shi ma da yake tabbatar da kai harin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Ayah ya ce binciken rundunar ya tabbatar da mutuwar mutum biyu kawai, ciki har da shahararren dan kasuwan nan da ke jihar Kogi mai katafaren shagunan da ake kira Chucks Supermarkets da ke birnin Lokoja, Mista Nicholas Ofodile.
Ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, CP Ayuba Edeh tuni ya tura jami’an tsaro zuwa yankin. Sai dai kuma ya kara da cewa kawo yanzu ba su samu cikakken bayanai kan lamarin ba.

Advertisement

labarai