A ranar Alhamis ce, ‘yan bindiga suka dawo babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama. An dan jima ba a samu ta’adin masu garkuwa da mutane a kan babban hanyar ba tun lokacin da aka saka dokar tafiye-tafiyen a tsakanin jihohi a cikin kasar nan sakamakon cutar Korona.
Ganau sun bayyana wa manema labarai cewa, wannan farmaki ya faru ne a kusa da kauyen Katari da misalign karfe tara na safiyar jiya Alhamis.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya daga wannan farmaki mai suna Mohammed Lawan ya bayyana wa manema labarai cewa, masu garkuwan sun fara farmakin matafiya wadanda ke kokarin shiga garin Kaduna ne da misalin karfe 8:50 na safe.
“Tsakaninmu da su bai wuce mita 250 sai muka hange su. Na hanga wata mota kirar Honda CRV 98 kofarta a bude kuma babu kowa a cikin ta, ashe sun yi garkuwa da matafiyan da ke cikin wannan mota ne.
“Mun ji karar bindiga lokacin da jirgi mai saukan angulu ta fara shawagi a wannan yanki,” in ji Mista Lawan.
Sai dai har lokacin rubuta wannan labara, ‘yan sanda ba su ci uffan ba game da wannan lamari.