Connect with us

TATTAUNAWA

Masu Sikila Miliyan 40 Ke Rayuwa Cikin kunci A Nijeriya – Kafi Liman

Published

on

Kowace ranar 19 ga Yuni ce Majalisar dinkin Duniya karkashinta na MDD ta ware, domin ta zama rana ta musamman ta yaki da cutar Sikila a fadin duniya bakidaya. A bisa haka ne Wakilin LEADERSHIP A YAU, KHALID IDRIS DOYA, ya tattauna da MUHAMMAD KAFI LIMAN, wani matashi wanda ya ke fama da cutar ta Sikila (Amosanin Jini) a Jihar Bauchi kuma shugaban gidauniyar yaki da cutar a karamar hukumar Shira, inda ya bayyana halin da su ke ciki, musamman na rashin kula da rayuwaru da gwamnatoci ke yi. Daga nan ya kuma tsawatar kan hanyoyin da su ka dace a bi, domin dakile matsalar. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ka gabatar ma na da kanka?
Sunana Muhammad Kafi Liman. Ni ne shugaban Gidauniyar ‘Sickle Cell Aid Foundation’ a Shira da ke jihar Bauchi.
A na bikin tunawa da ranar masu dauke da Sikila ta duniya, meye zaka iya cewa ganin cewa kai ma ka na da wannan cutar?
Sama da mutane miliyan 40 ne masu cutar Sikila da rayuwarsu take cikin hatsari, karkashin Gwamnatin Muhammadu Buhari. Sakamakon fama da karancin abinci mai gina jiki, tare da karancin sabbin magunguna na zamani.  Ina mika kokenmu zuwa ga Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, da cewar ya sani fiye da mutane miliyan 40 ne masu cutar sikila a kasar nan da suke cikin  mawuyacin hali na mutu kwakwai rai kwakwai, sakamakon matsanan ciyar yunwa da cutukan zazzabin cizon sauro a birane da karkara. Tare da karancin sabbin magungunan zamani na rage radadin cutar ta Sikila. Muna rokon Gwamnatin shugaba Buhari tare da Gwamnatocin jihohi, da Sarakuna iyayen kasa da su tausayawa majinyata masu cutar Sikila.
Sannan a na haifar masu cutar Sikila akalla mutane dubu 300,000 a shekara akan adadin da muke da su a kasa, fiye da mutane dubu 120,000 suke mutuwa a lokacin da aka haifesu, dubu 180,000 suke rayuwa cikin matsanancin hali sakamakon gazawar Gwamnatocin Nijeriya musamman Gwamnatin shugaba mai ci  Muhammadu Buhari, wajan kafa dokar tilasta yin gwajin aure a fadin Nijeriya.

Akwai kungiyoyi daban-daban da su ke fadi tashi kan wannan cutar baka da abun cewa a kansu?
A ce babu, muna dai mika kokenmu na nema taimakon gaggawa a karkashin Gwamnatocin duniya, musamman Gwamnatin Amurka da Birtaniya, da su taimaki masu cutar Sikila a Nijeriya da magunguna da kayan abinci masu gina jiki, tare da ilimantarwa akan gane illolin cutar ta sikila. Sannan muna sake mika kokenmu ga kungiyoyin cikin kasa dana kasashen waje, irin su CDC, Sabe The Children, UNICEF, WHO, FHI360, UN, UK AID, USAID, Doctors Without Borders, Action Against Hunger, IMF,  World Bank, da kuma European Union. Dukkanin kungiyoyinmu na cikin gida Nijeriya da za su iya taimaka wajen rage mana radadi gaskiya muna fatan su taimaka domin akwai ‘ya’yan talawa da suke dauke da wanan cutar basu da halin da za su kula da lafiyarsu. Kowa ya san cutar sikila tana matukar cin kudi da bukatar mai dauke da ita ake cin abinci na musamman. Su ma dadiaikun jama’a muna fatan za su dafa don yaki da wannan cutar.

Yanzu ka na son ka ce a wannan lokacin dukkanin gwamnatocin kasar nan ba su kula da bangaren wannan cutar?
Eh ba zan ce duka ba, domin a zahirin gaskiya gwamnatin jihar Kano tana sa’ayinta sosai don haka ne mu masu cutar sikila muke mika sakon godiya ta musamman ga Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, akan yaki da cutar Sikila da Gwamnatinsa ke yi. A Maiduguri ta jihar Borno muna isar da da sakon godiya ta musamman ga Gwamnatin Farfesa Zulum, bisa iya kokari da Gwamnatinsa ke yi akan ‘yan uwamu na sansanin ‘yan gudun hijira. Majalisar dokokin jihar Katsina da gwamnan jihar mun yaba da sa’ayinsu a kan masu cutar Sikila.
Baya ga su, a iya sanina akwai wasu daidaikun mutanen da suke bada gagarumar gudunmawa wajen yaki da cutar Sikila tare da taimaka mana ta fuskoki daban-daban zan bayyana kadan daga cikinsu domin karfafa musu guiwa kan wannan sa’ayi na alkairi irinsu kamfanin jaridun da suke daukar nauyin isar da kokenmu a duniya, musamman jaridar Leadership da suke taimakonmu akan yaki da cutukan Sikila, tare da ‘yan jaridan nan Khalid Idris Doyo, irin su Alh. Dahiru Muhammad, Alh.  Balarabe Alkassim Media Trust, Alh. Ishak Haruna  Hardawa Rediyo Nigeria, Allah ya saka musu da alkhairi, gaskiya sun bada gudunmawa sosai wajen yada halin da muke ciki a duk lokacin da muka bukaci hakan, don haka muke yaba musu a cikin bikinmu na wannan shekarar.

Ka yi ma na karin haske kan yadda ku ke jin radadin cutar?
Kamar yadda kowa ya sani ne, cutar Sikila wata cutace da take addabar mutane musamman yara, cutar tana tsananin azaftar da mu, duk yadda zan maka misalin irin tsananin da muke ciki za a dauka fadi ne a baki amma gaskiyar magana cutar sikila tana da hatsari sosai ga rayuwar al’umma. Cuta ce wacce za a sameta, uba bai huta ba, uwa ba ta huta ba shi kuma da an jefa shi cikin garari da zama abun tausayi. Don haka sakacin hukumomi a matakan karamar hukuma, jiha, da kasa kan nuna halin ko’inkula, shi yake kara rura wutar yaduwar wannan mummunar cuta  ta amosanin jini. Shin ko don cutar tafi kama ‘ya’yan talakawa ne da kuma mazauna karkara wadanda ba su da wayewar kai game da illolin cutar.
Kuma ni a matsayina na wanda wannan bala’i ya shafa ina ga kamar akwai taimakon hukumomi wajan kara yawaitar masu kamuwa da wannan cutar ta amosanin jinni wato (Sikila), sakamakon kin aiwatar da doka mai karfi a majalisar dokokin jihohi da kasa baki daya. Kasancewar ni da kaina duk da halin da nake ciki na je majalisar dokoki da gidan gwamnati wajen ganin gwamnati ta aiwatar da dokokin gwaji gabanin aure a fadin jiharmu ta Bauchi domin a ceto miliyoyin yaran da ba su kamu da wannan cutar ba. Kuma har yanzu ban daina bin duk hanyoyin da su ka dace mu bi don tabbatar da cewa gwamnati ta yi dokar tursasa gwaji gabanin aure, domin kawo karshen matsalar cutar sikila a tsakanin jama’a.

Ka hakikance kan gwaji kafin aure. Wane taimako hakan zai yi?
Rashin yin wannan gwajin shi ne ya sanya muma muka kamu da wannan cutar tun fil-azal, tuni masana suka gano cutar idan za a ke yin gwaji kafin yin aure ba za a kamu da cutar ba; idan aka tabbatar jinainan na miji da macen bai yi daidai ba; to wanda za a haifa zai kamu da hutar, in kuma yayi daidai to shi kenan za su iya yin aurensu. Domin wallahi mu masu wannan cutar muna matukar shan wahala, tun ina dan wata uku ake shan wahala da ni yau shekara 30 kenan ana fama da ni. Yanzu haka ma da kake ganina an min karin jini ne ya sanya ka ga ina wannan tafiye-tafiyen da har ka ganni na zo don na yi wannan kiran. Babu damar na yi tafiyar da ta wuce kilomita daya. Koda mashin na hau ko wani abun hawa sai na ji kirjina kamar ana daka. Yanzu haka iyayena sun yi nasu har sun gaji, masu taimaka min da jinni don na rayu sun ce sun gaji da me wannan yayi kama. Don haka maganar nan daya ce, a tursasa gwaji kawai ‘ya’ya su hudu da shan wahalar da ake kakaba musu.

Irin cutukar Sikilar su na da wani rabe-rabe ne?
Yanzu misali mu na da ire-iren cutukan amosanin jini wato sikila akalla guda tara (9): 1. Sickle cell anaemia; Na 2. Leukemia; na uku 3. Lymphoma; 4.Multiple myeloma; 5. Aplastic Anaemia; 6. Fanconi Anaemia; 7. Certain auto immune disease; 8. Myelodysplastic syndrome; sai kuma na karshe 9. Beta thalassemia major. Wadannan cutuka kala daban-daban har guda tara duk suna da alaka da rashin yin gwajin cutar amosanin jini wato sikila kafin yin Aure sakamakon gazawa tursasawa daga hukumomi a matakai daban-daban.
Duk da ya ke masana a kan masu binciken cututtukan da su ke da alaka a kan jini da bargo a jami’ar Harbard da ke kasar Amurka sun ce sauran cututtukan guda takwas sun fi alaka da cututtukan Cancer. Amma dai kiran da na ke yi ga ‘yan uwana na birni da karkara mutane su dage su fahimci kwayoyin tsatson halittar su wato ‘Genotype’ a turance kafin su kai ga yin aure, yin hakan kawai shi ne zai kawo rage kaifin masu dauke da irin cutar da mu ke ciki, kuma hakan zai kawo cigaba sosai wa kasa.

Ka dan kara bai wa jama’a ilimi kan cutar sikilar nan mana?
Ita kanta cutar amosanin jini (Sikila) ta kasu kashi hudu akalla. Ga su kamar haka: 1. Type SS wannan ita ce tafi kowacce irin cutar Sikila illa a cikinsu; 2. Type SC ita ce mai bin tafarkon; 3. Type AC mai bin ta biyu; sai kuma ta karshe 4. Type CC mai bin ta ukun. Duk da ya ke a cikin wadannan babu mai sauki magana ta gaskiya amma dai ‘Type SS’ ita tafi kowacce hadari ga dan adam, kasancewar duk sati biyu sai an yi  karin jini leda biyu ko uku.
Ni kaina da na ke amsa maka wadannan tambayoyin an saka min jini ya kai akalla leda 2,000 tun lokacin da aka haife ni zuwa yau shekaru 30. Kuma duk jerin wadannan cutukan da na jero idan kowacce maganinta ake bukata wuri mai saukin farashi ma sai an kashe kudin da ya kai miliyan takwas (8,000,000) a kasar India a Nijeriya kuwa sai an kashe kudin da ya kai miliyan 20,000,000, ana yin wannan aikin ne a jihar Ibadan ko Oyo, dole sai an kasha wannan kudaden kafin a maka dashen barko in a kasar Indiya ne zai kai miliyan takwas a Nijeriya kuma za ka iya kashe miliyan 20.

Yaya rayuwarka ke ingantuwa kenan?
Ai ba ni kadai ba, duk wanda yake fama da wannan cutar a cikin kuncin rayuwa yake rayuwa, kullum kana faman laulayi da ziyarta asibitoci, don haka muna rayuwa ne dafe-dafe. Akalla ni kaina na yi bara ko na ce ina yin bara da neman taimako a karkashi gwamnati jihar Bauchi da matakai daban-daban na gwamnati kasa da masu kudi akan a taimakeni a kaini asibiti a kasar India akan naira miliyan 8,000,000 har yanzu bukata bata biya ba ita wannan miliyan takwas din da ita ne za a yi wa mutum dashen bargo wanda halin da ko ni kaina nake bukata kenan. Ka ga akwai ire-irena da daman gaske da suke neman a agaza mana a fita da mu domin neman jinya.

Meye sakonka ga al’ummar Nijeriya?
Kasancewar tsananin halin da wannan cutar ke jefa yara da salwantuwar rayuka, domin idan wannan cutar ta samu dan talaka sai mutuwa fa, don wani lokaci alluran da za a sanya wa yaro ma gagara suke yi. Don haka ‘yan uwana inna kara rokonku kutseratar da milyoyin ‘ya’yayanku daga kamuwa da cutukan Sikila ta hanyar zuwa asibiti domin gwaji kafin yin aure. Idan masu son yin aure suka je asibiti aka yi gwajin kwayoyin tsatson halitta wato (Genotype) a turace aka samu kamar haka; da zan jero; Don Allah a hakura da yin wannan auran nan. Ga su kamar haka: SS+SC=Sikila; SS+AC=Sikila SS+CC=Sikila; SS+SS=Sikila; CC+SC=sikila; SC+SS+Sikila; SC+AC=sikila;  AS+SS=sikila;  SC+AC=sikila; AS+CC=sikila; AC+AS=sikila.
Wadanda kuma suka yi daidai babu matsala sune: AA+AA=Good; AA+SS=Good; AA+AS=Good; AA+SC=Good; AA+AC=Good; idan aka samu AA+CC ma ya yi daidai babu matsala za a iya aure hankali kwance.
Game da Genotype AS, su basa dauke cutar sikila, amma kuma za su haifi yara masu cutar,  AS+AS=SS,SS,SS,=AS,AS=AA. Ma’ana idan ma’aurata biyu suka hadu kowa yana da kwayar tsatson halitta Genotype AS+AS za a haifi yara uku masu cutar Sikila,  kuma za a haifi biyu wadanda za su haifi masu cutar sikila, sai kuma a haifi daya mai cikakkiyar lafiya.
Kuma ya kamata al’umma kowa ya san wanne irin jini Allah ya arzurtashi da shi, tunda muna da ire-iren jini ga su kamar  haka: 1. O+ O; 2. A+ A; 3. B+ B; 4. AB+ AB. Aji na farko wato Group O+ zai shiga O+ da O- da A+ da A- da B+ da B- da AB+ AB- duk yana shiga kowanne group. Sai group A+ zai shiga A+ da A-, sannan A- zai shiga A+. Sai group B+ zai shiga B+ da B-, sannan B- zai shiga B+. Sai group AB+ zai shiga AB+ da AB-, sannan AB- ya shiga AB+.
Wadannan sune ire-iren jini da muke da su wadanda aka fi sani a duniya, guda daya zai shiga cikin kowanne irin jini, amman sauran fa kowanne sai irin nasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: