Rabiu Ali Indabawa" />

Masu Sukar Gwamnatina Ku Rika Yi Da Adalci – Shugaba Buhari

Barazana Ga Tsaron Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci adalci daga masu sukarsa kan yadda yake gudanar da mulki, yana mai cewa ya kamata a rika la’akari da abubuwan da yake gudanarwa na ci gaban kasa.

Shugaban ya yi wannan bukatar ne a ranar Alhamis lokacin da ya karbi bakunci gami da sauraron Reberend Yakubu Pam, Sakataren zartarwa na Hukumar Zuwa Aikin Iabada Ta Kiristocin Nijeriya, a fadar Shugaban Kasa dake Abuja.A cewarsa, masu sukar su kasance masu adalci don la’akari da inda kasar ta kasance kafin zuwan Shugabancinsa, da kuma yanayin da take a halin yanzu, duk an saita al’amuran kan yawan kayan ayyukan da ake samu yau da kullum domin a yi aiki tare da kuma nasarar da aka samu tare da wadatar kayan aiki.

“Wadanda ke sukar gwamnatin ya kamata su zama masu adalci tare da yin tunani akan inda kasar take kafin zuwanmu, da kuma inda muke a halin yanzu, sannan wadanne irin albarkatu muka samar a yanzu da suke tare da mu.

“Dole ne mu yi gwagwarmaya wajen biyan bashi, saka hannun jari a gyaran hanyoyi da sake ginawa, don sake fasalin layin dogo da ƙoƙarin samun ƙarfi. Wannan shi ne abin da ni fata manyan mutane su yi la’akari da shi lokacin da suke so su yi amfani da dama wajen suka tare da kwatanta mu da gwamnatoci. ”A kan yanayin tsaro musamman a Arewa maso Gabas kuwa, Shugaban Kasar

ya yi tsokaci kan lamarin inda ya ce: “Yaya yanayin yake lokacin da muka zo? Idan aka yi dub ana nutsuwa ga al’ummar Jihohin Barno, Adamawa da kuma Yobe. Shin yaya yanayin kafin mu zo kuma menene halin da ake ciki a yanzu?

Har yanzu, akwai matsaloli a Borno da Yobe, a wasu lokutan matsalar Boko Haram, amma duk da haka sun san an samu bambanci, saboda da yawa jama’a sun fice daga jihohinsu sun koma Kaduna, Kano da kuma nan Abuja. Ba a bar mu da harin ba a wani lokaci, Gwamnati ita ce za ta yi aiki mafi kyau kuma ina fata cewa za’a samu mafi kyawun sakamako da zai gamsar. ”

Shugaba Buhari ya kuma ba da tabbacin cewa jin dadin ‘Yan Gudun Hijira a yanzu shi zai kasance mafi mahimmanci a cikin ajandar gwamnati.

Mutanen da ke sansanonin ‘yan gudun hijira, marasa karfi, tsofaffi,dukkansu ababen tausayine, ina tausayawa matasa saboda wannan shi ne lokacin da ya kamata su sami ilimi. Dole mu mu yi tsayin daka har sai wannan lokacin ya wuce, kuma ba mu sake yarda a dawowa da shi ba. Don haka muna farin ciki gami da sha’awar abin da ke faruwa a can na ayyukan jami’an tsaro, mu ma muna yin namu kokarin mafi kyau, “in ji Shugaban.

Ya yabawa Sakataren zartarwa kan nadin nasa da ayyukansa kan samar da zaman lafiya a duk fadin kasar duk da kankanin lokacin da yake da shi, kuma ya tabbatar masa da cewa kofar gwamnati a bude take a duk lokacin da yake da wata gudummawa da zai bayar.

Tun da farko a cikin jawabin nasa, Rabaran Pam ya ce ya yi kusanci da Shugaban a wasu daga cikin ayyukan hukumar, tunda aka nada shi a Yulin 2020. Wadannan sun hada da; Taron kungiyar zaman lafiya kan Kudancin Kaduna da kuma kokarin samar da zaman lafiya a Filato, Benuwai, Taraba da Jihohin Nasarawa.

Ya kara da cewa hukumar ta gabatar da shawarar karbar bakuncin Shugabannin addinan Kirista a cikin wani taron koli don taimakawa rage  matsin lamba a ciki da siyasa, a tsakanin sauran tsare-tsaren.

Exit mobile version