Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Gwamnan Jihar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce masu sukar matakin da gwamnatinsa ta dauka kan sauyawa wasu Kamfanoni fasali da cewa kauyawa ne. Ganduje ya yi wannan furucin ne kan sauya ginin Triump da Oyal din Daula zuwa wasu sabbin gine-gine domin ci gaba da amfanarsu. Ya ce wadanda ke sukar abinda Gwamnatinsa ta yi kauyawa ne kuma ba su yi binciken yadda zamani ke tafiya ba kafin tsoma baki kan batun.
Ganduje ya bayyana cewa masu sukar yadda Gwamnatinsa ta sarrafa wasu gine-gine ciki har da otal din Daula a matsayin kauyawa marasa hangen nesa.
Gwamnan na wannan furucin ne a yayin da ya ke duba aikin ginin birnin tattalin arzikin Kano da aka kasha Naira Biliyoyin naira wurin gina katafaren wurin da ke Dangwauro a kan titin Zaria kusa da birnin Kano cikin makon da ya gabata.
“Wadanda ke sukan mu ba su fahimci cewa aikin jarida na zamani baya bukatar babban gini domin wallafa jarida ba, hakan yasa zamu mayar da ginin gidan buga jaridar ta Triumph kasuwar canjin kudade na zamani.
“Masu canjin kudade na WAPA za su koma ginin kuma ‘yan kasuwar mu da dama za su amfana da wannan cigaban,” in ji Gwamnan.
Ya kara da cewa wadanda ke sukarsa ba su fahimci yadda aikin jarida na zamani ke tafiya ba inda ya bukaci su rika bincike kafin tsoma bakinsu cikin batu.
“Wannan ya nuna sun jahilci yadda ake aikin jarida na zamani. Ya kamata a tunatar da mutane cewa Gwamnatin da ta shude ce ta tilastawa jaridar Triump daina aiki kuma an dade da rufe kamfanin kafin mu zo mulki.
“Don haka su wane ke da laifi, wadanda suka kashe kamfani ko kuma wadanda suka fahimci muhimmancinsa suka dawo da shi?,” Inji shi.
Da ya ke magana game da Otal din Daula, Ganduje ya ce Ota din ya tsufa kuma baya tafiya da zamani. Don haka, zabin da ya rage wa Gwamnati shi ne ta fara amfani da shi, maimakon yin watsi da kadarorin al’umma.