Connect with us

LABARAI

Masu Zanga-zanga A Katsina Sun Kone Allunan Hotunan Buhari Da Masari

Published

on

Buhari/Masari

Wasu masu zanga-zanga a garin ‘Yantumaki ta karamar Hukumar Danmusa, a Jihar Katsina, a ranar Talata sun kona allunan da ke dauke da hotunan kamfen na Jam’iyyar APC, masu dauke da hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari.

Allunan da masu zanga-zangar suka kona suna kan babbar hanyar da ta shiga garin ne.

Masu zanga-zangar suna nuna fusatarsu ne a kan kara yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da kuma rashin tsaro a garin na sun a ‘Yantumaki da makwabtansa, inda suka bayar da misali da sace wani ma’aikacin lafiya mai suna, Alhaji Mansir Yusuf, da diyarsa wanda ‘yan bindiga suka yi da misalin karfe 1 na daren ranar ta Talata.

Hakanan masu zanga-zangar sun koka da kisan Hakimin garin, Atiku Maidabino, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga tantance ko su waye ba suka yi a cikin fadarsa.

Wasu ganau din sun shaida wa wakilinmu cewa masu zanga-zangar sun toshe babbar hanyar Katsina zuwa Kankara, inda su ke ta kona tayoyi a kan babbar hanyar da ta shiga cikin garin, wanda hakan ne ya tilasta wa masu motoci kauracewa bi ta babbar hanyar suna komawa da baya.

Masu zanga-zangar sun rika yawo ne daga wannan waje zuwa wancan a cikin garin suna iface-ifacen nuna kin jininsu da gwamnati a cikin harshen Hausa, inda su ke neman su ke neman gwamnatin da ta inganta harkokin rayuwarsu da dukiyoyinsu.

Duk da cewa an ga jami’an ‘yan sanda suna kai-komo domin tabbatar da zaman lafiya a garin amma dai har ya zuwa ranar ta Talata akwai alamun tashin hankula a cikin garin.

Rahotanni sun nuna cewa Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar ta Katsina, Sanusi Buba, ya umurci babban jami’in ‘yan sanda na yankin Dutsanma, Aminu Dayi, da ya koma garin na ‘Yantumaki da zama na wani lokaci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, SP Gambo Isah, ya ce, “Idonmu yana kan abin da ke gudana a garin, a yanzun haka ma akwai jami’anmu a cikin garin da su ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da kuma tabbatar da ganin masu zanga-zangar ba su dauki doka a hannunsu ba, ta yanda za a hana batagari jagorantar lamarin domin hargitsa garin ta hanyar kone-kone da satan dukiyar al’umma.

“Rundunar da sauran hukumomin tsaro suna kan lamarin domin tabbatar da an kama da hukunta wadanda suka aikata ta’asan baya-bayan nan na Kisan Hakimin garin da kuma sace jami’in lafiyan da diyarsa a ranar Talata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: