Masu Zuba Jari Daga Chana Sun Ziyarci Gwamna Ganduje

 

Daga, Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karɓi baƙuncin tawagar masu buƙatar zuba jari  daga Shandong Chana wanda  shugaban kamfanin Shandong Mr. Wen Younglin ya jagoranta,a lokacin ramakon ziyarar da Gwamna Ganduje ya Kaiwa wannan Kamfanin a kwanakin baya. Mr Younglin ya ce al’ummar Chana na da buƙatar zuba jari a ɓangaren harkokin rini, Noma, yawon buɗe ido, na’urorin zamani da kuma harkokin ciniki na zamani, sama da shekara 30 wannan lardi na Chana  ke fatan zuba jarin sama da Dala Miliyon 100 a ɓangarori daban daban a Jihar Kano.

Idan Za’a iya tunawa Gwamna Ganduje watannin biyu da suka gabata ya gudanar muhimman tattaunawa da mataimakin Gwamnan Shandong da kuma kamfanin Shandong Gold Mr. Younlin tare da wasu masu buƙatar zuba jari a ɓangarori daban daban wanda kuma hakan ne ya yi sandaiyya kawo wannan ziyara. Tawagar zata shafe kwanaki huɗu a jihar Kano wanda ae fatan zasu zaga ɓangarorin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, sannan kuma an shirya wata ƙasatacciyar walima gargajiya wadda Gwmana zai gudanar da baƙin na Jihar Kano.

A wani cigaban kuma Gwamnatin ta rabawa Ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano Miliyon 92,400.00 don ɗinka atamfun ziyarar zuwan Buhari, a shirye shiryen bukukuwan tarbar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa Jihar Kano ranar  litinin 27/11/2017, Gwamnatin Kano ta  baiwa Ƙananan hukumomin Jihar Kano 44 kyautar Naira Miliyon 2,100.000.00 kowacce, wanda idan aka haɗa jimlar kuɗin ya kama  Naira Miliyon 92,400.000. Kuɗin da aka Kira da Cotton Works an tura su  ga asusun  kowane shaguaban  ƙaramar  hukuma, bisa umarnin ya cire wasu adadi domin miƙawa wani jami’i da aka sakaya sunansa wanda kuma shi ake sa rana zai yi kwangilar ɗinka atamfun da za’a  sanya  a ranar bikin taren Buhari. Majiyar ta rawaito cewa an tura waɗannan kuɗaɗe tun makon da ya gabata.

 

Exit mobile version