Yusuf Shuaibu" />

Masu Zuba Jari Sun Yi Asarar Naira Biliyan 291.5 A Makon Jiya

Masu zuba hannun jari a Nijeriya sun yi asarar naira biliyan 291.5 a cikin makon jiya, an shaida cewa kasuwar hannun jari ta juya daga samun riba da nauyin tafiyar kasuwanci. An samu wannan asara ne duk da riban da wasu kamfanoni suka samu.
Wasu manazarta daga kamfanin ‘Afrinbest Securities Limited’ sun bayyana cewa, sun lura cewa samun riba da nauyin tafiyar kasuwancin ya samu matsin lamba ne a zango kasuwanci na kasuwan hannun jari a makon jiya, an auna nauyin kasuwanci guda hudu a cikin zango na biyar wanda ake samun guda 245 a kullum, inda aka yi asarar nauyin da ya kai biliyan 92.
A takaice dai, an samu asarar nauyin hannun jarin na biliyan 90 a kasuwancin banki ranar Litinin. A ranar Talata, an samu nauyin kasuwancin na miliyan 102 a cikin bangarorin kasuwancin guda uku. A ranar Laraba an samu nasarar maido da nauyen kasuwanci na biliyan 15 daga hannun masu sayar da kayayyaki.
An samu asarar faduwar hannun jari ne a ranar Alhamis, lokacin da aka samu asarar nauyin kasuwanci na biliyan 47 daga hannun kasuwancin banki. An samu raguwar samun rabar kasuwancin hannun jari a cuikin makon jiya, ribar ya sauka zuwa nauyin kasuwanci na biliyan 22 ranar Juma’a inda ya kara karfafa asarar, shi ne mafi girman asara da aka samu cikin mako zuwa mako.
Manazartan daga kamfanin Afrinbest sun bayyana cewa, biyo bayan asarar da aka samu cikin makon jiya, ana tsammanin za a samu kasuwanci da wuri cikin wannan mako. Sun ce, bayar da kananar takardun hunnun jari wanda masu zuba jari da kasashan waje suka yi, zai ta a samu abin da ake tsambani.
Yawan hannun jari na biliyan 1.113 wanda kudin sa ya kai naira biliyan 13.465 na kasuwancin 15,036 wanda masu zuba hannun jiri suka zuba a makon jiya, wanda ya bambanta yawan dukkanin hannun jari na biliyan 1.290 wanda kudin sa ya kai naira biliyan 13.873 na kasuwancin wanda aka gudanar na makonni da suka gabata na kasuwancin 17,307.
Yawan kudin da aka auna na hannun jarin biliyan 926.286 wanda kudin sa ya kai biliyan 9.696 na kasuwancin 9,906, duk da haka ya taimaka da kasha 83.25 da kuma 72.01 na duka yawan kudin kadara.
Masana’antar watsa labarai ta hayar kimiya tana da hannun jarin miliyan 73.076 wanda kudin say a kai naira miliyan 14.664 na kasuwancin guda 35. Masana’anta ta karshe mai yawan hannun jarin miliyan na miliyan 36.749 wanda kudin sa ya kai naira biliyan 2.562 na kasuwanci 2,301.
Manyan kamfanoni guda uku masu hannun jari sun hada da FBN Holdings Plc, Zenith Bank Plc da kuma Diamond Bank Plc, wadanda suke da hannun jari na miliyan 551.865 wanda kudin sa ya kai naira biliyan 6.602 na kasuwancin guda 3,116, sun taimaka da kasha 49.60 da 49.03 na yawan kadarorin kasuwanci.
Hakazalika, duka sauran kamfanonin sun samu asara, ban da kamfanoni kananan kasuwanci da na kamfanonin mai masu kasha 0.21 da 0.09.
Kamfanoni 18 sun yaba da farashi na makon jiya, kasa da 24 na makonnin baya, yayin da suka samu karancin farashi 45, sama da 37 wanda ake samu a makonnin baya.
Manyan kamfanoni wadanda suka samu riba wannan mako su ne, Cap Plc, Mcnichols Plc, Royal Edchange Plc, Cadbury Nigeria Plc da kuma UACN Property Debelopment Company Plc, wadanda suka samu ribar kashi 10, 9.62, 9.37, 9.09 da kuma kashi 7.14.
Manyan kamfanoni wadanda suka yi asara sun hada da Africa Prudential Plc, FCMB Group Plc, Zenith Bank Plc, International Breweries Plc da kuma Wema Bank Plc, inda suka yi asarar hannun jarin da ya kai kasha 20.83, 12.74, 11.82, 10.92 da kuma kashi 10.47.

Exit mobile version