Abubakar Abba" />

Masu Zuba Jari Sun Yi Kididdigar Asararsu Ta Watan Janairu, Sun Kuma Ci Ribar Naira Biliyan 806

Masu zuba jari a kasuwar sayar da hannun jari ta kasa su yi kididdigar asarar da suka tabka data kai ta naira biliyan 326 a cikin watan Janairu da kuma cin ribar naira biliyan 806 a cikin kwanuka 15.
Kasuwar ta samu ragi sama da sau biyu a cikin rabin shekara a ranar 9 ga watan Janairu ganin cewar, hada-hadar ta kasuwar ya sauka zuwa naira tiriliyan 11 daga naira tiriliyan 11.72 a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2018.
A cikin wannan watan masu zuba jarin sun samu riba tun daga cikin watan Yulin shekarar 2017.
Kudin kasuwar ya kai naira tiriliyan 11.384 a ranar 31 ga watan Janairu, inda ya kai naira tiriliyan 12 a ranar 12 ga watan Fabirairu sun kuma kara karu zuwa naira tiriliyan 12.2 bayan da aka gama cin kasuwar a ranar juma’ar data wuce.
Masu yin fashin baki a kamfanin Meristem Securities sun bayyana cewar, kasuwar ta kasa samun yawan masu zuba jari kafin zuwan ranar gudanar da zabubbukan shekarar 2019 .
Acewar su, hada-hadar a kasuwar ta karu a yan kwanukan baya saboda yakinin da masu zuba jari suke dashi, inda hakan ya santa suka shiga kasuwar gadangadan .
Kasuwar ta ci gaba da bunkasa a zagaye na hudu dana biyar a satin da ya gabata, inda ta rufe akan 376 ganin cewar dukkan shiyar ta karu daga kashi 3.76 zuwa kashi 32,715.20 na bps, inda had zuwa yau, ta kai kashi +4.09 bisa dari.
Yawa da kuma hada-hadar da aka yi a kasuwar ta karu daga kashi 49.68 bisa dari zuwa kashi 4.66 bisa dari, inda kasuwar ta daidaita zuwa akan 2.76d, tare da samun wadanda suka ci nasara su 58 sai kuma wadanda suka yi asara su 21.
Fannin mai da iskar gas da kuma kayan da akayi hada-hadar su, anyi kokari sosai, inda aka samu bps 594 da kuma bps guda 541 daga sari zuwa sari, musamman kamfanin mai na Oando Plc dana kamfanin mai na Seplat Petroleum Debelopment Plc, 11 Plc, Unileber Nigeria Plc, Cadbury Nigeria Plc da kuma kamfanin Nigerian Breweries Plc.
Kayan da masana’antu suke sarrafawa sune sukazo na uku wajen samun nasara, inda ta kai ta bps 162 daga sati zuwa sati duk da bps 10 na asarar da akayi a ranar juma’ar data gabata bayan da kamfanin Dangote na siminti da kamfanin Lafarge Africa Plc suka tsallake yin asarar a simintan su harda kamfanin sarrafa siminti na Arewacin Nijeeiya.
Bugu da kari, fannin banki ya samu ribs yar kadan data kai ta bps 159 daga sati zuwa sati bayan da Bankin Union Bank Nigeria Plc da bankin , Ecobank, kamfanin Transnational Incorporated, bankin United Bank for Africa Plc da kuma Zenith Bank
Plc suka tsallake yin asara, harda bankin Guaranty Trust Bank Plc da kuma Access Bank Plc.

Exit mobile version