Mata Ba Su Iya Bai Wa ‘Yan’uwansu Mata Kuri’a A Nijeriya – Jakadan Australiya

Daga Zubairu M Lawal Lafia,

Jakadan kasar Australiya a Nijeriya, John Donnelly ya bayyana damuwarsa kan yadda mata ba su cin moriyar da ta kamata a Nijeriya musamman wajen samun mukamai na shugabanci.

Ya kara da cewa tsarin mulkin Nijeriya ya ba mata damar tsayawa takarar kowani mukami tun daga matakin kujerar shugaban kasa da gwamna da kuma majalisa, amma abin bakin ciki a duk lokacin zabe matan da ke tsayawa takara ba su wuce kashi goma cikin dari kacal ba, kuma masu yin nasara a zabe ba su kaiwa kashi uku da digo takwas.

A cewarsa, sau da yawa mata sun fi maza fitowa kada kuri’a a dukkan zabubbukan Nijeriya, amma ana samun karancin mata da ke tsayawa takarar zabe. Bugu da kari, ya ce matan ba su iya bai wa mata ‘yan’uwansu kuri’a mafi rinjaye.

John Donnelly, ya bayyana haka ne a wajen taron kara wa juna sani da wayar da kai wanda sashin yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya a birnin Abuja cikin makon da ya gabata.

Ya ce mata suna samun moriya kadan ne a siyasar Nijeriya bayan an kafa gwamnati a kan ba su mukamai kasa da kashi goma sha shida a cikin gwamnati mai makon nasu ya fi yawa ko ya zo daidai da wanda aka bai wa maza.

Daga karshe ya bukaci mata da su rika jurewa suna tsayawa takarar manyan kujeru da kanana daga matakin tarayya har zuwa jiha da kuma kananan hukumomi.

Exit mobile version