Rabiu Ali Indabawa" />

Mata Biyu Sun Zama Alkalan Manyan Kotu A Jihar Yobe

Jihar Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya rantsar da wani Mukaddashin ‘Grand Khadi,’ Babagana Mahadi, Alkalan Babbar Kotuna biyu da Khadi guda biyu na Kotunan Shari’a, a ranar Asabar, a Damaturu, babban birnin jihar.

Gwamnan ya bayyana taron a matsayin wani mahimmin ci gaba wajen sake sanya bangaren shari’a da kuma gabatar da adalci a cikin sauri a jihar, yana mai cewa nade-naden sun yi daidai bisa cancanta.

“Nadin shugabanninsu, Mukaddashin Grand Khadi, alkalan babbar kotun da Khadi na kotunan Sharia an yi su ne bisa cancanta kuma daidai da karfin da aka bani.

Wadannan, ya ce sun yi daidai da Sashe na 174 karamin sashe na biyu, sashe na 27 karamin sashe na 2 da kuma na 276 karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin 1999 na Tarayyar Nijeriya, kamar yadda aka yi masa kwaskwarima.

Sauran wadanda aka rantsar sun hada da Alkalan Babbar Kotun mata biyu, Hadiza Musa da Amina Shehu, tare da Khadi biyu na Kotun Shari’ar, Khadi Bashir Inuwa da Khadi Abba kime.

Buni ya yi kira ga sabbin wadanda aka nada su ba da hujjar amincewa da su, yana mai cewa: “Yayin da muke murnar nadin naku, bari na tunatar da ku da sauri cewa ana bukatar abubuwa da yawa daga gare ku don ba da hujjar wadannan nade-naden.

Buni ya ce “Ya kamata a yi hakan ta hanyar gudanar da ayyukanka cikin gaskiya da adalci ga kowa da kowa, ba tare da banbancin siyasa, tattalin arziki, addini ko kabilanci ba, domin bangaren shari’a ya kasance shi ne fatan karshe na talaka.”

Exit mobile version