Mata Da Masu Karamin Karfi Suka Fi Fuskantar Barazanar Kamuwa Da Cutar Kansa —Bincike

Wani sabon bincike da kamfanin Phillips Consulting ya yi ya bayyana cewar halin da ake ciki na matsalalolin da ake fuskanta wadanda suka shafi tattalin arziki da kuma zamantakewa, wanda kuma hakan ne yasa mata, da kuma wasu masu karamin karfi suka kasance daga cikin wadanda matsalolin da suka shafi cutar kansa, tafi shafuwar su a Nijeriya.
Shi dai wannan binciken ya samu gudunmawa ne daga wadanda suke fama da cutar ta Kansa a Nijeriya, sai kuma wadanda suke kula da lafiyar su, iyalansu da kuma abokanni, wannan kuma ya nuna cewar yawancin al’ummar Nijeriya suna tafiya ne zuwa kasashen waje, saboda su samu wuraren da suke da asibitoci masu kyau wadanda za’a duba lafiyarsu kamar yadda ya kamata.
“ A kasar Nijeriya kafofin yada labarai suna cikin farin ciki, sun kuma gamsu da rahotannin da suke samu dangane da wadanda suke fama da cutar kansa, da kuma kokarin da suke yi na neman taimako, saboda su je kasashen waje wajen neman maganin cutar wadda take da matukar hadari musamman wadanda suke fama da ita.
“ Akwai cibiyoyin kulawa da lafiya na masu fama da cutar kansa a Nijeriya, wadanda basu yin wani al’amarin daya shafi maganin cutar,, hakanan ma Hukumar kula da inshorar lafiya ta kasa, kudaden da ake biya saboda samun maganin kansar a Nijeriya abin ya fara ne daga Naira N850, 000 zuwa fiye da Naira milyan N3.6m.
“ Tunda yake yawancin ‘yan Nijeriya ba za su iya biyan wadannan kudaden maganin cutar kansa ba, saboda tsadar da suke da ita, shi yasa ma yanzu yawan wadanda suke bukatar a taimaka masu a cikin shekarun da suka wuce yake karuwa. Hakan kuwa tana faruwa ne saboda matsanancin tsada saboda haka ne yawancin ‘yan Nijeriya ba za su iya sayen su magungunan ba. Hakan kuma shi yasa wadanda suke neman taimako suke karuwa,a shekaraun da suka wuce, wannan ma wata manuniya ce wadda kuma ta ke nuna irin matsalolin da ake fuskanta wadanda suka shafi zamantakewa da kuma tattalin arziki wadanda masu cutar kansa suke fuskanta,. da kuma masu kulawa da su, kamar dai yadda wadanda suka yi binciken suka bayyana.
Kamar dai yadda aka yi wani bincike a shekarar 2015, yawan mace- macen da ake samu a sanadiyar cutar kansa abin ya karu da kashi 17 tsakanin shekarar 2005 da kuma 2015, nan kuma da shekara ta 2030 al ‘amarin kansa a fadin duniya ana sa ran zai karu da kashi 68 , zuwa sababbin wadanda ake sa ran za su kamu da cutar, zuwa miliyan 23.6 a ko wacce shekara.
Babban jami’i kuma Shugban kamfanin Phillips Consulting, Mista Bictor Mba, shi ikirari ya yi da Hukumomi masu zaman kansu, cewar su hada kai da gwamnati, saboda a dauki matakan da suka kamata dangane da yadda za’a ga karshen cutar kansa.
“ A cikin shekarar 2012 cutar kansa tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da milytan 2 a Nijeriya, wadannan bayanan an samo sune daga kokarin da ma’aikatar lafiya take yi da kuma kungiyoyi masu zaman kan su, sai kuma masu bincike daban -daban , ga kuma wadanda suka nuna sha’awar su ta taimakawa, lokaci ya yi da za su yi hakan tunda dai taimakon ana neman shi matuka. Cutar kansa tana sanadiyar mutuwar mutane fiye da milyan 2 a Nijeriya.
“Hakanan kuma idan har da gaske ake yi ana yakar cutar ne, a kuma tabbata sai an rabu da ita, saboda haka sai a samu daukar wasu matakai, wannan kuma duk masu ruwa da tsakani dangane da shi al’amarin,. ba kawai za’ayi shiru ba ‘ wannan kuma ba wai kawai ana neman tsaida shi al’amarin akan binciken ba, saboda a kawo karshen cutar kansa ba, an ma shirya ma taimakawa wadanda suke da ruwa da tsaki ba. Bugu da kari kuma ya kara jaddada cewar a shirye suke su taiamaka ma kungiyoyi masu zaman kansu. Hana nan ma a shirye suke su taimaka ma wadanda suke da ruwa da kuma tsaki da cewar su tabbar da an dauki manyan matakai akan shi al’amarin yadda za ‘a samu ingantattun hanyoyi yadda za’a lura da maganin cutar kansa ta tsare-tsaren da za’a gabatar.

Exit mobile version