Mata Da  Matasan Kogi Sun Amfana Da Shirin  Noma Na APPEALS

Daga Abubakar Abba

 

Aikin noma na (APPEALS) a jihar Kogi ya fara rabar da kudade ga mata da matasa a jihar da suka amfana da aikin donin a kara tallafa masu wajen gudanar da aikin na Noma.

Aikin na  APPEALS ne ya samar da hanyar samo kudaden domin rabawa wadanda suka amafana da aikin domin su fara gudanar da aikin noma domin samun riba.

Har Ila yau kuma,  aikin an kirkiro da shi ne,  domin kara samar da da ayyukan yi,  nusamman a tsakanin mata da matasa da kuma kara bunkasa tattalin arzikin na wadanda suka amfana da aikin a jihar.

Bugu da kari,  kafin a rabar da kudaden ga wadanda suka amfana,  sai aka tabbatar sun yi rijista  da hukumar yin rigista kasuwanci  ta hanyar bude asusun ajiya a bankuna tare da kuma amincewar shirin zuba jari na bankin dub ya ta hanyar aikin na APPEALS .

A cewar Jami’in aikin na  APPEALS a jihar Dakta  Sanni Abdullahi Ozomata,  “Ina mai bai wa wadanda suka amfana da aikin cewa,  dole ne a hada hannu wajen maido da kudaden da aka ba su domin sima na baya su amfana”.

Jami’in Dakta   Sanni Abdullahi ya ci gaba da cewa, an gudanar da bayar da kudaden ne bayan wadanda suka amfana sun yi rjista,  sun bude asusun ajiya a bankuna tare da kuma ambuncewa  kan tsarin  zuba jari domin yin kasuwanci.

“ Sai da aka gudanar da bayar da kudaden ne bayan wadanda suka amfana sun yi rjista,  sun bude asusun ajiya a bankuna tare da kuma ambuncewa  kan tsarin  zuba jari domin yin kasuwanci.Bugu da kari,  Dakta   Sanni Abdullahi,  a wata gana wa da shirin na  APPEALS ya shirya nasu ruwa da tsaki,  domin ganin an wanzar da shirin karfafa wa mata da matasa gwiwa  (WYEP),  ya  bayyana cewa, makasudin tattanawar shi ne,  donin a  kara wayar da kan wadanda za a yi aikin da su a karkashin shirin biyo bayan kudaden da aka rabar wa wadanda suka amfana. “

Dakta   Sanni Abdullahi ya  kara da cewa,  ganawar ta zama wajbi,  musamman domin wadanda za su gudanar da aikin su san ana tare da su,  musamman  kan ayyukan da  suka shafi wadanda suka amfana da aikin yin noma domin riba.

“ Ganawar dole ce  musamman domin wadanda za su gudanar da aikin su san ana tare da su,  musamman  kan ayyukan da  suka shafi wadanda suka amfana da aikin yin noma domin riba.”

A cewar Dakta   Sanni Abdullahi, abin takaici ne ga wadanda suka shafe watanni suna samun horo kan shirin daga bisani   kuma  suje suna sayar da kayan da aka ba su tallafi domin yin kasuwancin na noma.

“Abin takaici ne ga wadanda suka shafe watanni suna samun horo kan shirin ssnnan kjma suje suna sayar da kayan da aka basu tallafi domin yin kasuwancin na noma. “

Ya kuma sgawarce su da suyi amfani da damar Da suka samu na horon da kuma tallafin domin su zamo masu dogaro da kawunan su.

 

Abdullahi ya kuma koka kan yadda wasu masu gabatar da aikin ke hada baki da wasu da  suka samu horon wajen canza aikin,  inda  ya yi gargadi da cewa, shirin ba zai lamunci aikata dukkan nau’ukan damfara  daga gun wadanda suka amfana da kuma masu gudanar da aikin ba.

Ya kuma yu kira a gare su da su tabbatar ds sun kiyaye dukkan ka’idojin da aka gindaya na aikin,  musamman domin kawace yin amfani da kudaden da aka ba su ba a bisa ka’ida ba

Dakta   Sanni Abdullahi ya ba su tabbacin cewa,  Jami’oin shirin  na APPEALS  da ke daukacin jihohin kasar nan,  za su ci gaba da ganin an wanzar da shirin a Jihohinsu domin a yiwa kowa adalci.

Exit mobile version