Zuwaira Mohammed Bako ‘yar boko, ma’aikaciyar gwamnati, sannan kuma ‘yar kasuwa, ta shawarci mata da su tashi tsaye wajen koyon sana’a, sannan kuma kada a raina ko yaya take. Zuwaira ta bayyana haka a cikin tattaunawarta da shafin Adon Gari, gad ai yadda hirar ta kasance.
Da farko masu karatu za su so jin cikakken sunanki, da sunan da aka fi sanin ki da shi.
Sunana Zuwaira Mohammed Bako, amma an fi kirana da Umma Zuzu ko Maman Junainah
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
To ni dai haifaffiyar Maiduguri ce, can aka haife ni, na yi makarantar firamare a nan, sai na yi karatun sikandire a Bauchi (FGG bh), daga nan na koma Maiduguri don matakin karatu na gaba
Kamar wacce irin sana’a kike yi?
Kamar yadda na ce sana’o’i muna da kamfani ne wato ‘AlphaTree multi business bentures, so kin san shi ina Kek, muna turaren wuta, muna gyaran jiki, muna harkar buga takardu printing, muna sai da garin danwake da yajin tafarnuwa
Kin samu kamar shekara nawa da fara wannan sana’a?
Sana’ar garindawanke muka fara Tun 2015, sai 2017 muka fara sayar da turaren wuta, Sai gyeran jiki, da yin abincin gidan biki da dangogin cincin ‘snacks’. Sai 2020 muka fara sana’ar printing.
Me ya ja hankalinki har kika fara sana’ar?
kawata ce ta ja hankali na muka fara shi, wato sana’ar sayar da garin danwanke, take bani labarin yadda abin ke tafiya kamar ana so sosai, sai ta ce mu hada hannun jari mu fara, kuma Alhamdulillah.
Kafin ki fara ita sana’ar da kike yi, shin kin nemi shawarar wasu don neman sanin yadda ake yin ta, ko zuwa kikai aka koya miki, ko dai kawai farawa kikai da kanki?.
gaskia ban nema ba, akasari kawata ce ta ce mu gwada a kan zaman gida da muke ba aiki lokacin ba ‘ya’ya kin san duk muna amare, sai shafin snacks gaskiya ba’a koya min ba da kaina na koya, haka zalika gyaran jiki, sai na turaren wuta ne aka koya min. Shi kuma printing wata baiwar Allah ce ta ce da ta ga yadda nake gyara gashina, ta ce wa yake min, na ce wata ne, ta ce gaskiya ya yi kyau ai zama in fara sana’ar,
na ce to bari mu gwada.
A ina kika koyi ita sana’ar.
Gaskiya garin dawanke yi mana ake har yanzu, sauran kuma kamar yadda na ce a ba ya bangaren turaren wuta da kaina na koya.
Ya karbuwar sana’ar ta kasance wajen su masu sayen kayan, kasancewar shi ne farkon farawar ki a lokacin?.
Wallahi ya karbu sosai, kin san garin dawanke kayan marmari ne, haka zalika turaren wuta da gyeran jiki Sabida an san ni ‘yar maiduguri ce shi ya sa ya karbu sosai shi ma.
Yanzu haka kusan ko wacce shekara, mu kan bi abokan huldarmu mu ji ta inda muka gaza, idan sun fada sai mu karo neman ilimi kan wannan abin da ake samun matsala sai mu gyara..
A ina kike gudanar da ita sana’a, shin kina da wani waje ne na daban da kika ware don ita sana’ar ko kuwa a cikin gida kike yi?
Fannin abinci a gida, Gyeran jiki kuma muna yi yanzu a spa din kawata, gaskia yawanci dai a gida muke yi a bangaren gyaran jiki yanzu
Daga lokacin da kika fara ita wannan sana’ar har kawo iyanzu, wanne irin nasarori kika samu game da ita?
Gaskiya da yawa, said ai godiya ga Allah.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta game da sana’ar, musamman ga masu sayen kayan?.
Masu daukan bashi su ki biya, a nan muke fuskantar kalubale
Ko akwai wadanda kike koyawa sana’ar, idan babu, shin kina da sha’awar koyawa wasu?.
Akwai su na kan koyar da fannin Kek, da gyaran jiki da humra, shi kuma turaren wuta ban fara ba gaskiya, mai yiwuwa nan gaba.
Wacce shawara za ki ba wa mata na gida musamman wadanda suke zaune kawai ba tare da wata sana’a ba?
Zamani ya canja a tashi a kama sana’a musamman matan aure, zaman haka ba zai yiyuwa ba, kuma kar a raina ko wace irin sana’a idan an dan samu jari a kama sana’a a juya taro da sisi.
Idan kika ci karo da matan da suke zaune a gida ba sa wata sana’a ya kike ji a cikin zuciyarki?.
Ko kina da wata shawara ko dan tsokaci da za ki gaya wa sauran ‘yan uwa masu sana’a?.
Akwai, Allah ya sake hada kanmu, sannan garemu masu sana’a iri daya, mu daina gasa da juna ko gaba kana bin da bai da tushe kowa rabonsa ya ke ci.
Me zaki ce ga makarantar wannan shafi ?
Aikinku yana kyau, mun gode da wannan damar da kike bamu muna magana har a ji, sabida ta wannan hayar muke zaburar da juna har wasu su ji shawa’awar fara tasu sana’ar.
Me za ki ce da ita kanta jaridar LEADERSHIP A Yau?.
Aikinu yana kyau sosai, sannunku da aiki, mun gode da wannan dama