Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Gwamnatin Kano ta sake yaye wasu matasa guda 550 waɗanda suka sami horo a fannoni daban- daban na sana’o’in hannu domin dogaro dakai.
Da yake jawabi a wajen taron yaye matasan da aka gudanar a gidan Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin
Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje. Kwamishinan ƙananan hukumomi na jihar Kano. Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana cewa, tun zuwan wannan Gwamnati ta Ganduje ake horas da matasa a fannoni iri daban-daban na sana’a dan su dogara da kansu. Ya zuwa yanzu an yaye dubbai tare da tallafa musu da kayan sana’a da jari.
Cikin Matasan 550 da suka sami cin gajiyar horaswar da aka yaye akwai mata da aka koya wa aikin gyaran famfo da sauran fannonni. Alhaji Murtala Sule Garo ya yi kira ga matasan da su yi kyakkyawan amfani da tallafinda aka ba su ta yin sana’ar da suka koya dan tallafa wa kansu da kuma al’umma. Ya yi kira ga matasan su kula da irin kishin da mai girma Gwamna yake a kansu su zama abin misali ta dogaro a kan sana’o’in da aka koya musu dan tabbatar bunƙasar arziki a jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.