Daga Mahdi M. Muhammad
Mutane 11 da aka sace wadanda aka saki a daren Talata sun bayyana cewa, mata su na kawo mu su abinci sau biyu a kowace rana a inda aka yi garkuwa da su na tsawon mako guda.
An yi garkuwa da su mako guda da ya gabata a kan hanyar karamar hukumar Ekrerabbwen Ughelli da ke Arewacin titin gabas ta yamma na hanyar Warri da ke Jihar Delta, inda wasu da a ke zargin ‘yan daba ne su ka kama su.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da shi wanda ya yi magana a Warri, a karkashin sharadin sakaya sunansa ya bayyana cewa, wadanda suka yi garkuwar da su a wannan ranar bai nuna cewa suna harin wani ba. Sun zo kan hanya ne da yammacin ranar don yin garkuwa da mutane koma su wanene. Sun kuma bude wuta kan motoci, kuma motocin da suka tsayar da mutanen an yi garkuwa da su,” in ji shi.
Da yake ci gaba da bayyana faruwar lamarin, wanda ya kubutar ya ce, mako guda da suka yi a hannun masu satar mutanen sun buge su don ganin sun kira abokai da dangi don neman kudin fansa na sakin su. Wasu daga cikin dangin wadanda aka sace sun iya biyan kusan naira dubu dari biyar don sakinsu.
A cewar wanda aka azabtar, an yi garkuwa da su kusan mutane ashirin da wannan yamma, ya kara da cewa, sai suka kasa su kashi biyu zuwa sansanoni daban-daban.
“Masu satar ba su da wasa ko kadan. Abin da kawai suke so shi ne kudi. Suna da mata wadanda ke kawo mana abinci sau biyu a rana. A cikin duka mutanen da suka sata sun samu kudi mai yawa a matsayin kudin fansa kafin a sake mu,” in ji shi.
Wadanda aka saki din sun bayyana cewa, an rufe musu idanu kuma an bi da su ta cikin koguna zuwa inda aka sare su na tsawon mako guda. A can masu satar mutanen za a gansu sanye da abin rufe fuska kuma suna dauke da muggan makamai.