Mata Ku Mallaki Mazajenku Ta Hanyar Biyayya -Siyama Khalid

Mata

MataSiyama Khalid matar aure ce, wacce ta fahimci cewa ladabi da biyayya ga miji domin neman zaman kafiya shi ne mafita, in ta shawarci mata magidanta da su yi kokarin mallakar mazajensu ta hanyar yi musu biyayya, domin a cewarta zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Siyama ta yi wannan bayani a hirarta da shafin adon Gari, kamar yadda za ku karanta kamar haka.

Masu karatu za su so sanin cikakken sunanki da tarihinki a takaice

Assalamu alaikum, sunana Siyama Khalid, ni haifaffiyar ‘yan garin Bauci ce amma ina zaune a Niga na yi makaranta ta a Niga wanda a nan na gama sakandirena.

Shin Malama Siyama matar aure ce?

Eh ni matar aure ce.

Ya kike gudanar da rayuwar auren ki a cikin gidan ki?

Eh gaskiya ina jin dadin zama da mijina saboda muna zaune da mijina lafiya ba hayaniya, sannan kuma akwai kwanciyar hankali tsakani na da mijina, yana nuna min so ni ma kuma ina nuna masa so, baya bukatar ganina cikin bacin rai ko kuma a ce shi ne ma zai yi sanadiyar bacin raina babu wannan, gaskiya ni dai babu abin da zan ce sai dai na gode wa Allah don na yi sa’ar miji nagari mai sona da gaskiya da amana ina gode wa Allah da ya hada ni da shi.

Malama Siyama kina da ‘ya’ya?

Eh Ina da ‘ya’ya.

‘Ya’yanki nawa?

Su uku ne, maza biyu mace daya.

Ko zaki iya gayawa masu karatu kadan daga cikin yadda kike gudanar da tarbiyya yaranki?

Eh gaskiya ina kokari ni da mijina wajen ganin tarbiyyar ‘ya’yammu ta inganta, muna basu kulawa sosai wajen ganin sun samu cikakken ilimi na addini da na boko, to daidai gwargwado mijina yana iyakar kokarinsa wajen ganin ‘ya’yan nan ba su neman abu su rasa tun daga kan kayan zuwa makaranta har zuwa ma’amalarsu da yara zuwa abubuwan de rayu gaskiya ba ma cewa komai sai de Alhamdulillah Allah ya saka wa mijina da alkhairi.

Malama Siyama kina wata sana’a ne ko kuma ke ma’aikaciya ce ko kuma kina zama ibada ne?

A’a bana sana’a, sannan kuma ni ba ma’aikaciya bace ina zaman aure ne.

Kina zauna ne a gida kika ce ganin yadda yanayin gari ya canja kowa ya tashi zuwa neman na kansa ba kya sha’awar yin wani dan kasuwanci ne saboda kina samun dan canji a hannunki ko kuma maigidanne ba ya so kin san ba kowane namiji ne yake son ya ga matarsa tana sana’a ba?

Eh toh gaskiya haka ne ba wai sana’ar ce bana son yi ba daga mijina ne gaskiya ba ya son hayaniya ko kuma na ce fitina shi ya sa, maganar canji kuwa gaskiya bana rasa kudi a hannuna saboda mijina baya barina ba kudi, yana iyakar kokarinsa gaskiya, to kin ga idan ya hana ni sana’a ma ai yana da hujja, saboda ban nema na rasa ba shi ya sa ma kin ga idan ya hanani sana’a dole ba zan yi ba.

Ba ki fada mana matakin karatun ki ba?

Eh gaskiya bayan na gama sakandire na yi aure, amma gaskiya ina son yin karatu kuma ban fidda rai ba, saboda ba abin da na ke so irin na ga na zama likita in sha Allahu shekaran nan mai zuwa zan koma makaranta don yanzu haka ma ina shirye shirye ne.

Wanne irin kalubale kike taba fuskanta a cikin rayuwar zaman aurenki?

To a gaskiya ba zan ce ban taba fuskantar kalubale ba, ba kuma zan ce na taba fuskanta ba saboda a rayuwa ba za ka ce ba ka samu abin da ba ka so ba, sannan kuma ba za ka ce ka samu abin da kake gaba daya ba.

Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu a rayuwar zaman auranki?

Nasara kam ba’a magana, babu nasarar da ta kai ka samu namiji adali a wannan zamani irin mijina, nasara a rayuwar zaman aure babu abin da ya kai zaman lafiya ni dai a ganina, sannan kuma ban nemi komai narasa ba ina karkashin kulawar mijina, bayan nan kuma Allah ya ba ni haihuwa to babu nasarar da ta kai wannan.

A da can da kike karama menene burinki?

A gaskiya na yi burin cewe ba zan yi aure ba sai na gama karatuna, to amma kinsan dayake kana naka Allah yana na sa, Allah ba haka ya so ba, amma na Allah shi ne daidai haka shi ya fi zama alkhairi.

Wanne abu ne yafi faranta miki rai a kan rayuwarki ta gidanki.?

Ina jin dadin na ga sanda mijina zai dawo na kammala komai nawa daga kan shara, girki, gyare-gyaren gida na shirya ‘ya’yana sannan kuma ni ma na shirya kaina na yi tsaf ina jiran mijina ya dawo, saboda idan ban kammala wani abu ba mijina ya dawo ba na jin dadin haka, sai na ga duk inda raina yake ya baci zan ga to duk me nake yi tun safe har mijina ya dawo ina yi wani abu, ba zaman jiransa ba.

Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?

Ina so mutane su rika tunawa da ni da alkhairina da kuma kirkina saboda ba’a mantawa da mutum mafi alkhairi da mai kirki.

To yanzu idan kika fara karatu, ga karatu ga kuma yaranki da mijinki, tayaya zakina basu kulawa kamar yadda kika saba.?

Wannan in sha Allahu ba zai gagara ba zan san yadda zan yi na tsara komai ya tafi yadda nake so ba wata matsala in Alllah ya yarda.

Idan kika fara karatu za ki zama ga karatu ka kuma hidimar gida da yara da kuma mijinki, ta ya yi ne za ki samu damar gudanar da hutunki?

To daman idan mutum yana karatu ai baya samun wani hutu, sannan kuma akwai Asabar da Lahadi ranar da ba’a zuwa makaranta ko.

Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?

Ina so a ce min Allah ya yi miki albarka.

Wanne irin goyon baya kika samu a wajen mijinki na niyyar fara makaranta da za ki yi, ma’ana za ki ga wasu mazan ba sa son Matansu su tafi karin karatu?

To ni dai Alhamdulillah, gaskiya mijina bai hana ni zuwa karin karatu ba, hasali ma shi ne ya wuce min gaba wajen neman gurbin karatu.

Wace irin shawarwari kike samu daga wajen kawayanki a kan zamantakewarki ta aure?

A gaskiya bani da wasu kawaye da nake wata magana da su akan gidana, saboda yanzu idan ba ka yi sa’ar kawaba ka je kana kwashe sirrinka kana gaya mata ba lallene ta iya rike maka sirri ba saboda haka ni ba wadda nake magana da ita ta haka.

Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?

Gaskiya ina so doguwar riga, don yanzu haka dogowar riga ta fi yawa a cikin kayana.

A karshe wace irin shawara za ki ba wa ‘yan uwanki mata?

Shawarar da zanbawa ‘yan uwana mata shi ne suyi kokari su mallaki mazajensu ta hanyar biyayya, domin a azuna lafiya, zama lafiya ya fi zama dan sarki in ji Hausawa.

 

 

Exit mobile version