Connect with us

ADON GARI

Mata Ku Tashi A Dama Da Ku Bangaren Ilimi Da Sana’o’i –Fatima Gwadabe

Published

on

FATIMA GWADABE ‘yar Jarida ce da take aiki aiki a gidan Talabijin na Arewa 24, ta yi kira ga mata masu mike kafa komai sai dai miji, ‘yan uwa su yi musu komai, da su farka daga baccin da suke yi su fito a dama da su ta fannin ilimi domin a yanzu duniya ta sauya, ba ni-ba ni bas hi da wani alfanu ga rayuwar mace. Fatima Gwadabe ta yi wannan kira ne a tattaunawarsu da wakiliyar LEADERSHIP A Yau Juma’a,…. ga yadda hirar ta kasance.

Masu karatu za su so su ji cikaken sunanki da cikaken tarihin rayuwarki

Sunana Fatima Rabi’u Gwadabe. An haifeni a garin kano, na yi karatuna tun daga Firamare zuwa jami’a a garin kano. Na karanci fannin koyon aikin jarida (Mass communication) a jami’ar Bayero, na yi wa kasa hidima a jihar Jigawa, na kammala a kano. A halin yanzu ba ni da aure, ina aiki ne gidan talabijin na Arewa24. Amma kuma, na koyi aikin lokacin ina makaranta (Internship), a shekarar 2011 a Freedom Radio Kano, sannan kuma a Edpress Radio kano (NYSC) a 2014. Bayan na kammala na fara aiki da Arewa24.          

 

Ta yaya kika fara wannan shiri na ‘Akushi Da Rufi,’ kuma meye ya jawo ra’ayinki kika fara wannan shirin?

Kafin Akushi da Rufi, akwai shirin girki da nake gabatarwa mai suna ‘Muna Kwarya,’ dake karkashin sashin ‘Gari Ya Waye’ na Arewa 24, wanda shi ne shirin girki na farko a tashar. A lokacin da bukatar samun sabuwar mai gabatar da shirin ‘Akushi da Rufi’ ta taso, Jagorar shirin ta shawarce ni da ni ma na yi rubuta takarda ta nema tunda ina da kwarewa akan harkar girki, da kuma gabatar da shirin girkin, a lokacin bani da masaniyar ni ma ina da damar neman shirin, tunda tuni ina ganin ina da shirin na girki da nake yi. A takaice dai wannan shi ne yadda na fara ‘Akushi da Rufi’ tsawon watanni shida kenan yandu.        

 Mece ce ma’anar ‘Akushi Da Rufi’ kuma me ya sa kuka zabi wannan sunan?

A matsayina na mai gabatar da shirin, idan muka dauki ma’anar a Hausa a dan karamin ilimin da nake da shi, kwanon abinci ne da ake sassakawa mai rufi na alfarma da ake yi wa kwalliya, wanda sarakai da manyan mutane ke amfani da shi, musamman a zamanin da, har ake masa kirari da “Akushi da Rufi’ sai Sarki”. Idan muka juya kuma bangaren shirinmu, Akushi da Rufi yana nuna nau’ikan girke-girke na musamman marasa wahalarwa, wadanda wasu idan ka ji sunayensu za ka yi zaton za su ba da wahala (Rufin kenan), amma sai ka shiga shirin sai ka ga sabanin haka. A turance dai ina cewa girke-girke da suke ‘Unikue but not complicated.’

Ta yaya kuke samun masu zuwa su dafa abinci a wurin, ko kuna gayyatar mutane ne?

Muna gayyatar wadanda muka sani, sannan wasu ana tattaunawa da su, wasu suna kawo kansu ta hanyoyi shafukan sada zumunta, wasu ta bangaren ‘yan’uwa, abokan arziki, abokan aiki da dai sauransu.

To Yanzu kai tsaye idan ana son zuwa shirin, wace hanya ya kamata a bi?

Ta hanyoyin da na fada a saman kowanne tabi za ta samu dama. Sannan ba mata kadai shirin yake karbar bakuncinsu ba, har da maza, sharadi shi ne bakon ko bakuwar su kasance masana a kan harkar girki (chef or caterers) da kuma mashahuran mutane (celebrities).

Idan har mace za ta zo shirin, ita za ta zo da kayan abincinta Ko yaya ake yi?

Kayan abinci mu ne muke samarwa, muna ba wa bakinmu damar su zabi nau’in abincin da suke so su ilimantar da masu kallonmu da shi, sai su turo mana kayan hadin abincin, da yadda ake yi, mu kuma za mu duba don mu tabbatar ya yi daidai da tsarinmu. A yanzu dai ba mu fara ba, kuma akwai matasan masu yin girki da yawa da idan muka fara da su zasuyi matukar ba da mamaki, ba wai a dahuwar kadai ba, wanda kuma hakan zai zaburar da sauran yara.

Sau tari za ki ga akwai wasu Mata da ba su damu da karatu ba ko Sana’ar yi wane kira za ki yi ga irin su?

Baza’a ce mata ba su damu da sana’a ko karatu ba, sai dai a ce wasu daga cikin sun yi sake an yi gaba an barsu a baya. Mata da dama yanzu sun mike sun jajirce wajen neman rufawa kansu asiri, yanzu zamani ya canja, ko in ce duniyar ma ta canja gaba daya. Duk da haka dai zan yi kira ga wadanda suka mike kafafu ba sa yin komai da su tashi su ma a dama da su ta bangaren ilimi da sana’a, har yanzu suna da dama, lokaci bai kure musu ba. Komai kankantar sana’a kada a raina ta, kada ki ce da kin fara sana’a kike so ki yi kudi lokaci guda, dole sai an saka hakuri da jajircewa, a hankali har ki kai ga matsayin da wasu suka taka. Ba wai ga matan aure kawai ba har ga marasa auren, yawan bani-bani ga miji, iyaye, ko ‘yanuwa ba shi da alfanu.

Wane sako za ki aika wa masoyanki masu kallon Akushi da Rufi?

Ina matukar godiya gare su, wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina kaunarsu, Allah ya bar mana zumunci, amin.

Mun gode sosai da hadin kan da kika ba mu

 Ni ma na gode.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: