Abubakar Abba" />

Mata Manoma Sun Kammala Taron Yini Guda A Zariya

Kungiyar mata manoma da suka fito daga shiyya ta daya a jihar Kaduna, sun jagoranci taro na musamman, inda suka tattauna mas’aloli da suka shafi ci gaban noman da suke a tsakaninsu.

A jawabinta a matsayin shugabar kungiyar, Hajiya Asibi Sabon Garin Zariya, ta fara bayyana cewar, sun shirya taron ne domin bayyana wa mambobinsu ayyukan da suke aiwatarwa, domin tallafa wa mambobin, na yadda za su sami dangwalen kayayyakin noma daga gwamnatin tarayya da sauran cibiyoyi da suke da alaka da tallafa wa manoma a ciki da wajen Nijeriya.

Hajiya Asibi ta kara da cewar, kungiyar ta yi-ruwa, ta yi- tsaki, na tsaya wa mata da yawan gaske inda suka sami rancen kayayyaki da kuma kudade a bankin raya noma a tarayyar Nijeriya.

A nan sai ta yaba wa wadanda suka amfana, na yadda suke bin ka’idodin da aka tsaya a kansu,

aka ba su dangwalen.

Sai dai kuma Hajiya Asibi ta nuna matukar damuwar ta na yadda gwamnatin jihar Kaduna, ba ta cusa mata manoma a cikin tsare-tsaren da ta ke yi, da ya shafi bunkasa noma a fadin jihar Kaduna Kaduna. Da kuma Hajiya Asibi ta juya ga mambobin kungiyar a shiyya ta daya, sai ta yi kira garesu, da su, da su ci gaba da hada kansu, na yadda za su amfana da duk wani tsari na tallafa wa mambobin wannan kungiya, da shugabannin kungiyar suka bankado.

Shi ko shugaban wannan taro, kuma shugaban kungiyar manoma a jihar Kaduna Alhaji Nuhu Aminu, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda mambobin wannan kungiya suka hada hannu, suke Magana da murya guda, a karkashin wannan kungiya ta manoma mata a shiyya ta daya a jihar Kaduna.

Alhaji Nuhu ya lashi takobin yin duk abin da ya dace, na ganin tsarin da kungiyar manoma da ya ke yi wa shugabanci a jihar Kaduna, an sa su a cikin tsari, ta yadda noman da mambobin wannan kungiya ke yi, su ma sun amfana da noman da suke yi, fiye da yadda suke amfana a halin yanzu.

A dai jawabinsa,Alhaji Nuhu Aminu ya ce, kafin faduwar damunar bana, wannan kungiya, a karkashin kungiyar manoma ta jihar Kaduna, za su samar ma su da Tan-Tan, wato motar nomad a iraruwa ma su inganci da kuma takin zamani da za su biya a cikin sauki, wannan, a cewarsa, zai matukar tallafa ma su, na yadda za su bunkasa noman da suke yi a halin yanzu da kuma nan gaba.

A dai lokacin wannan taro, bako mai jawabi, Malam A.S,Bello, malami a kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Zariya, ya jawo hankalin daukacin manoma mata da suke wannan kungiya da su hada kansu, su guji duk wata gutsuri-tsoma da za ta iya zama silar rabuwar kansu, in sun dauki wannan mataki, a cewarsa, a dan lokaci kadan za su sami ci gaban da kowa zai mamaki.

Suko wakilan ‘yan majalisar Birnin Zariya da kuma mazabar waje, Alhaji Kasim Iliyasawa da kuma Dan Asabe Cokali, wakilan sun ce, ‘yan majalisar da tsare-tsare ma su yawan gaskeba za su aiwatar das u ba, sai sun cusa wannan kungiya a ciki, kuma wannan alkawari zai cika kafin faduwar damunar bana.

Sauran shugabannin wannan kungiya ta manoma mata a shiyya ta daya da suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Hajiya Murjanatu Danjuma da kuma Uwar-gida Helin, inda dukkansu suka yi bayanai ma su yawan gaske na yadda kungiyar ta tashi tsaye, na fafutukar ganin sun bi duk hanyoyin da suka da ce, domin ci gaban manoman da suke cikin wannan kungiya.

Exit mobile version