Jummai Ibrahim" />

Mata Mu Taimaki Kanmu, Rayuwar Yanzu Ba Wanda Ta Bari

Malama Hauwa Ahmad, mace ce da za a iya buga misali da ita ta fuskoki da dama musamman a bangaren neman na kai. Ta gwanance wurin sana’ar sarrafa abinci na kwalam da makulashe iri-iri na zamani. Bayan haka, jaruma ce da ta yi tsayuwar daka wajen taimaka wa zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma inda ya kai ga ta kafa Kungiyar Taimakon Al’umma ta musamman domin daukaka zaman lumana. Wani abu da zai ba jama’a mamaki shi ne ta yi wannan duk kokarin ne bayan aurenta yam utu wanda wasu na iya tunanin watakila tun da babu namijin da zai tallafa ma ta, ba za ta kai gaci ba. A wannan tattaunawar da muka yi da ita, ta yi wa mata tsaraba tare da karfafa musu gwiwar tashi-tsaye su nemi na kai, domin a cewarta rayuwar yanzu babu wanda ta bari. A karanta hirar tun daga farko har karshe domin jin abubuwan da ta bayyana.

Da farko ki bayyana wa masu karatu takaitaccen tarihin rayuwarki…

Ni dai sunana Hauwa Ahmad, an haife ni a garin Kaduna a Unguwar Shanu, na yi primary school dina (makarantar firamare) a NDA. Sannan na yi secondary (sakandare) dina a Kano United, Kachako. Sai na yi aure a shekarar 1996, ina da yara hudu, uku maza mace daya, na rabu da mijina shekara hudu da suka wuce.

 

Malama Hauwa da alama kasuwanci kike yi, ko za ki fada mana wane irin kasuwanci ne sannan me ya sa kika zabi yin sa?

To ni dai mace ce mai son girke-girke don haka nake sana’ar kicin, wato na dafe-dafe da toye-toyen kayan kwalama iri-iri. Unguwar da nake suna bukatar wadannan abubuwan na kayan kwalama. Sannan kuma duk girman unguwar babu irin wadannan abubuwan na kayan kwalaman. Shi ne na zauna na yi tunanin ya kamata na tashi na taimaki ‘yan’uwana mata da suke cikin unguwar. Abin da za ka je kasuwa ka siyo ga shi a kusa da gidanka ko babu komai an samu saukin kudin abin hawa.

 

To su wadannan kayayyakin da kike siyarwa kina hadawa da danye ne ko dai wanda mutum zai zo ya cika tumbinsa ne kawai ya yi gaba?

A’a, ba wanda mutun zai cika tumbinsa ba ne. Sai dai idan mutun na bukata akwai lambar waya sai ya kira don a soya mashi kamar irin marasa mata haka.

 

Wane kalubale kika taba fuskanta kan wanan sanaar?

 

Kalubale, eh to kasan shi Dan Adam ajizi ne duk inda ka kai ga iyawa wani za ice baka iya ba. Amma da taimakon Allah muna tsallake duk wani kalubale idan ya taso cikin sauki.

 

Kince Yanzu ba ki da aure, shin kina da sha’awar sake wani auren nan gaba?

(Dariya sosai), aure nufi ne na Allah, duk inda na kai ga son shi sai Allah ya kawo, Alhamdulillah ina maraba da zabin Allah.

 

Bayaga wanan sana’ar na sarrafa abinci, shin kina wani aiki ne daban ko makaranta kike yi?

A’a, ba na yin karatu yanzu sai dai mu taimaka yara su ma su yi. Ba na aiki sai dai ina wani NGO (Kungiyar Taimakon Al’umma Mai Zaman Kanta). NGO din akan zaman lafiya ne kuma mun samu karbuwa sosai, mun kuma kai ga cin nasara sosai a Kaduna da ma Nijeria baki daya. Wannan NGO din mun sa ma ta suna “Nigeria Peace Adbocacy” wanda wani Bawan Allah mai son cigaban kasa yake jagoranta, sunanshi Yusuf Ali Rabagardama, a halin yanzu yana neman kujerar Sanata a Mazabar Kaduna ta Tsakiya. Muna rokon Allah ya bashi sa’a amin. Akwai mutane da dama wanda idan na ce zan fade su gaskiya zan cika muku ko ina da sunayensu.

 

Wani kira za ki yi ga matan da ke rungume hannu komai sai dai su jira miji ya ba su?

To, A gaskiya duk macen da take haka ba ta so taimakon kanta ba, a yanzu ma babu irin wannan matan gaskiya, kowa kanta ya waye. Idan ba ki yi don mijinki ba to ai kya yi don yaranki.

 

Ko akwai wani abu da kike so ki fada wa masu karatu da ba mu tambaye ki ba?s

E to, babu sai dai a kullum ina ba wa mata ‘yan’uwana shawara da cewa da su tashi su taimaki kansu da kansu da zuriyarrmu, rayuwar yanzu babu wanda ta bari.

 

Mun gode da hadin kai da kika ba mu.

Ni ma nagode, Allah ya ba smu sa’a baki daya, ku ma da kuke kara wayar mana da kai Allah ya taimake ku baki daya. ‘Yan’uwana mata ba a raina sana’a, yanzu fa babu maraya sai rago, nagode.

 

 

Exit mobile version