MATA SAI DA ADO

Mace a koda yaushe ita ’yar kwalliya ce. Wannan ya sa mu ka ware fili guda, domin koya wa mata kwalliya. Wato ado na jiki, gami da tsaftar jikin shi kansa. Ita mace ba ta tsufa muddin ta na raye matudar kullum a cikin kwalliya ta ke.

Akwai kwalliya ta hanyar gyaran ga shi, walau kitso; wato gyaran gashi.

Kunshi ma ya na kara wa mace kyau. Lalle kuma ya na yiwa mata magani ta wasu bangarorin, amma fa zallar lalle; ba wai irin wanda a ke kwabawa, domin yin zane-zane a kafa ba.

Shi ainihin lalle ya na yiwa mata magani sosai a jiki. A na gyaran jiki da shi, a na kuma gyara gashi da shi.

Ita kwalliya da a ke ganin ta ta kasu kasha-kashi. Ya kamata uwar gida ta fahimci a koda yaushe akwai yadda a ke yin kwalliya. Akwai kwalliyar safe kafin maigida ya fita, akwai kwalliyar rana, akwai kuma ta dare.

Kowacce ya kamata mace ta san yadda za ta ringa yiwa maigidanta kwalliya ba tare da gundurar da shi ba. Haka bangaren saka tufafi shi ma akwai salon saka tufafi na kowanne lokaci ta yadda mace za ta kayatar da maigida.

Amma kafin wannan, tsafta ta na da matukar muhimmaci ga mu mata. Tsafta ta kasu kashi-kashi. Tsaftar tsakargida kanta, tsaftar falo, tsaftar dakin kwanciya da kuma tsaftar madafa, wato dakin girki. Sai uwa uba bandaki.

Mace ta san yadda za ta gyara gidanta lungu da sako wajibi ne. Ita ma ta san yadda za ta tsaftace jikinta tun daga kanta har kafafuwanta, kana ta san yadda za ta tsabtace baki, kunne, hanci, da sauransu.

Sannan ta san yadda za ta tsaftace tufafinta. Mace ta san yadda za ta kuma tsaftace ’ya’yanta. Ta san irin shigar da za ta ringa yiwa yara lokacin zafi da lokacin sanyi ko damina. Wannan zai taimakawa yara inganta lafiyarsu. Insha Allah za mu ringa kawo muku, kwalliya da adon mata kasha-kashi daidai da kowanne yanayi.

Mu hadu mako mai zuwa!

Exit mobile version