Zubairu M Lawal">

Mata Sun Taka Muhimmiyar Rawar Yaki Da Korona, In Ji Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Mista Antonio Guterres, ya yabaw a rawar da mata suka taka a lokacin yaki da Korona.

Babban Sakataren ya bayyana hakane a ranar bukin yara mata ta Duniya ta ya gudana a ranar 11 ga Oktoba, 2020.
Mista Antonio Guterres ya ce Majalisar dinkin Duniya ta ware wannan ranar ce domin tunawa da rayuwar yan mata masamman wadanda suke rayuwa cikin kunci.
Babban Sakataren ya ce sau dayawa mata suna tsuntar kansu cikin wani hali na kuncin rayuwa. Yayin da wasu KE stuntar kansu cikin aikin bauta mara tushe.
Sakataren ya ce dole a rika wai wayawa domin duba halin da suke ciki da kuma taimaka masu masamman kananan yara da ake sanyasu cikin muguwar rayuwa.
Antonio Guterres ya ce mata suna taka rawa wajen ganin cigaban al’umma a ko ina cikin kasashen Duniya.
Ya ce rawar da mata suka taka wajen wayar da kan al’umma a lokacin da Duniya ta shiga cikin wani hali na kuncin rayuwa saboda yadda annobar cutar Korona bairus ya dakufe harkokin Duniya.
Mata sun kulla da rayuwar yara kanana a lokacin da aka kasance cikin kulle a gida.
Sannan yayi kira ga Gwamnatocin Duniya da su bai wa mata kulawa wajen samun ilumi mai inganci wanda zai taimakawa rayuwar su.
Mata su taka rawa a dukkan fannoni na rayuwar dan Adam. Ya kasance duniya ta na damawa da su wajen cigaba a bangaren kimiyya da fasaha da sauran abubuwan cigaba.

Exit mobile version