Mataimakan Firai Ministar Birtaniya Sun Fara Shirin Kamfe Na Ko Ta Kwana

Kafar dillancin labarai ta Reuters ta rawaito hadiman Firai Ministar Birtaniya Theresa May, sun fara shirye shiryen ko ta kwana na kamfe din zabe wanda za’ayi a watan Nuwamba, domin ta tsira da aikinta da kuma shirin fitar Birtaniya, daga tarayyar turai a wani rahoto da Jaridar Sunday Times ta wallafa.

Jaridar ta ce, manyan jami’an biyu na siyasa dake ofishin Firai Ministar a Downing Street, sun kaddamar da shirin atisayen kamfe din zaben domin samun nasarar goyon bayan al’umma a sabon shirin, bayan an caccaki shirin da ta mika na fitar Birtaniya daga tarayyar turai a taron kolin da akayi a Salzburg, a makon da ya gabata.

Ya zuwa yanzu ofishin Firai ministar bai ce komai ba game da wannan rahoto.

 

Exit mobile version