Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya gana da babbar ministar kudin Birtaniya Rachel Reeves jiya Lahadi a birnin Landan, inda suka zurfafa musaya game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudade, da sauran batutuwan dake janyo hankulan kasashensu.
He, wanda kuma shi ne ya jagoranci tawagar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki da harkokin cinikayya tsakanin Sin da Birtaniya, ya ce kamata ya yi kasashen biyu su yi aiki tare, wajen aiwatar da muhimman kudurori da shugabannin kasashen suka cimma, su kuma ingiza nasarar dandalin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Birtaniya, da zurfafa musaya da hadin gwiwa a dukkanin sassan tattalin arziki da cinikayyarsu, da ingiza cimma moriya tare, da wanzar da nasarori, da ci gaba da daidaita bunkasar alakarsu ta fuskar raya tattalin arziki.
A nata bangare kuwa, Reeves wadda ta jagoranci tawagar Birtaniya a tattaunawar, cewa ta yi bangaren kasarta na dora muhimmancin gaske ga hadin gwiwa da Sin, kuma a shirye yake ya karfafa tattaunawa, don aiwatar da sakamakon tattaunawar tattalin arziki da harkokin cinikayya tsakanin Birtaniya da Sin, da shigar da sabon kuzari ga hadin gwiwar tattalin arzikin sassan biyu. (Saminu Alhassan)