Sagir Abubakar" />

Mataimakin Gwamna Ya Nemi A Dinga Yada Labaran Gaskiya

Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, ya shawarci masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani da su tabbatar da cewa duk labaran da suke sanyawa ingantattu ne kuma sahihai ne.

Alhaji Mannir Yakubu, ya ba da wannan shawarar ce a lokacin da ya amshi bakuncin wakilan Katsina city news, whatsapp group, da suka kai masa ziyara.

Ya bayyana cewa, yanzu kafafen sadarwa na zamani sun zama wani bangare na aikin jarida a wannan zamani na kimiyya, wanda al’umma na amfani da shi sosai.

Alhaji Mannir Yakubu, ya yaba da irin kokarin wakilan kafar sadarwar ta Katsina city news whatsapp group din, na tsaftacewa tare da sanar da al’umma al’amurran da suka shafi kasashen ketare tare da kuma game da ba da shawara ga gwamnati a kan ababen da suka shafi al’umma.

Ya sha alwashin hada hannu da su don ciyar da jihar Katsina gaba.

Alhaji Munnir Yakubu, ya yi kira a gare su da su nemi a rika horar da mambobin su game da aikin jarida na yanar gizo.

Tun da farko, Admin din group na jihar, kuma tsohon shugaban ma’aikata na jihar Katsina, Alh. Lawal Aliyu Daura, ya ce, sun zo ofishin Mataimakin Gwamnan ne tare da yi ma shi gaisuwar barka da Sallah tare da gode ma shi game da yanda ya baiwa kafar na su mahimmanci.

Ya ce, manufar kafar shi ne ta ilmantar, ta nishadantar tare da sanya kyakkyawan dangantaka tsakanin al’umma da gwamnati.

Sauran da su ka yi magana a wajen sun hada da, SA Restoration, Alh. Sabo Musa Hassan, Hajiya Bilkisu Muhammad Kai-kai, Alhaji Ibrahim Dalhatu Makudawa, Danjuma Muhammad Katsina, wanda shi ne admin na group da sauransu.

Exit mobile version