Daga Haruna Akarada
Mai Girma Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, wanda Alhaji Musa Yusuf Yawale (Tafidan Gama) tare da Manajan Darakta na Hukumar Karota, Baffa Babba Dan’Agundi, su ka wakilta wajen cika alkawarin da ya yi wa wani dattijon dan Karota, Malam Mansur Suleman Dawakin Kudu, inda ya gwangwaje shi da sabon gallelen babur (Roba-roba) kirar UD.
Dr. Gawuna ya yi alkawarin ba wa dattijon babur din ne a wajen taron karramawa da kungiyar masu aike wa da labarai (Kano Correspondents Chapel) su ka shirya ranar Asabar din da ta gabata a otel din Bristol Palace ga wasu zakakuran mutane, wadanda shi kanshi Mataimakin Gwamnan ya na cikin wadanda a ka ba wa lambar karramawar kuma shi ma dattijon ya na cikinsu.
Kungiyar ta karrama dan Karotan ne bisa kwazonsa, inda duk da shekarunsa sun ja, amma idan ya zo aiki har dare ya ke kai wa kafin ya tashi daga inda ya ke bada hannu, wato kan titin Iyaka Road.