Haruna Akarada" />

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Je Ta’aziyyar Tsohon Kwamishinan Shari’a Na Jigawa 

Ana cigaba da jajantawa iyalan marigayi Jastis Muktar Adamu wanda Allah ya yi wa rasuwa a wannan makon. Marigayi Alhaji Adamu, tsohon kwamishinan shari`a ne a Jihar Jigawa, ya rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya, a cewar Zannan Kazaure wanda shi dan me rike da sarautar Zannan Kazaure.

Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya wakilci Gwamna Drakta Abdullahi Umar Ganduje zuwa Unguwar Nassarawa G.R.A don yin Ta’aziya ga iyalai da yan’uwan Marigayin, mai shekaru 74, wanda mahaifi ne ga Zannan Kazaure, Architect Muhammad Mukhtar.
Mataimakin Gwamnan, ya yi Addu’ar fatan Allah ya jikansa da sauran al’ummar Musulmi baki daya. Haka abin ya ke ga ‘yan uwa da abokan arziki da Jami an gwamnatin Jihar jigawa duk sun halarci wannan gida domin yin ta aziyya ga Zannan da sauran iyalansa.

Exit mobile version