Mataimakin Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Sumaila a majalisar, Hon. Zubairu Hamza Masu, tare da takwaransa mai wakiltar kananan hukumimin Shanono da Bagwai, Hon. Ali Ibrahim Isa Shanono, sun fica daga Jam’iyyarsu ta APC zuwa Jam’iyyar NNPP.
‘Yan majalisar biyu sun bi sahun sauran takwarorinsa da ke zauren majalisar dokokin Kanon, inda suka rubuta wa shugabannin mazabunsu takarar ficewa daga jam’iyyar APC saboda dalilansu da suka bayyana.
- 2023: ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano 3 Sun Kara Ficewa Daga APC Sun Koma NNPP
- 2023: ‘Yan Majalisar Dokokin Kano 9 Sun Fice Daga PDP Zuwa NNPP
‘Yan majalisun dukkansu suna kokawa ne kan yadda aka gaza bawa demokradiyya hakkinta a jam’iyyance tare da rikice-rikicen cikin gida da ya dabaibaye Jam’iyyar tasu.
Kazalika sun koka kan hanyar da aka bi wajen fitar da ‘yan takarar gwamna da mataimaki da wofantar da bukatarsu a siyasance.
Ko a makon da ya gabata wasu ‘yan Majalisa akalla guda 9 ne suka yi kaura daga Jam’iyyar PDP zuwa NNPP, sai kuma karin uku daga APC zuwa NNPP, ga karin biyu yau.
Yanzu dai NNPP tana da wakilai akalla guda 15, sai wakilin Tarauni na PDP guda 1 rak, APC kuma ke da wakilai 24.