Mataimakin Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Kamfanin Dillancin Labaru Na AP

Daga CRI Hausa

A kwanakin baya, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya zanta da babban direktan kula da watsa labaru na kamfanin dillancin labaru na AP dake yankin kasar Sin Ken Teizo Moritsugu.
A yayin intabiyun, Le Yucheng ya bayyana cewa, yanzu duniya na cikin yanayi mai cike da babban canji, wanda ba a samu irinsa ba cikin shekaru dari daya da suka gabata ba.
Ya ce a matsayin su na kasashe dake da karfin tattalin arziki mafi girma a duniya, yadda ake raya dangantaka tsakanin Sin da Amurka yana da muhimmanci sosai. Kuma tilas ne a daidaita dangantakar su.
Kasar Amurka ta kara mai da hankali ga fannin yin takara, da nuna adawa da juna, kan dangantakar dake tsakaninta da Sin, amma ta mai da hankali kadan ga hadin gwiwarsu, wannan ra’ayi ba shi da inganci sosai, ya kuma kaucewa burin samun ci gaba.
Ya ce babu shakka, ba za a iya magance takara a tsakanin manyan kasashen biyu ba, amma ya kamata kasashen biyu su yi takara cikin zaman lafiya, maimakon nuna kiyayya da juna. A matsayin manyan kasashen biyu masu nauyi a wuyensu a duniya, ya kamata Sin da Amurka su yi watsi da nuna kiyayya da juna, musamman ma su magance rikicin da aka tada da gangan. Ya ce ya kamata kasashen biyu su fadada hadin gwiwarsu, wanda ta haka ne za su iya kara samun moriyar juna. (Zainab)

Exit mobile version