Abba Ibrahim Wada" />

Mataimakin Mourinho Zai Rabu Da Mourinho A Karshen Wannan Kakar

 

Rui Faria, mataimakin Mourinho da suka shafe shekaru 17 suna aiki tare a matsayin mai koyar wa da mataimakinsa ya bayyana aniyarsa ta barin Manchester United a karshen wannan kakar bayan an kammala gasar FA Cup ta kasar Ingila.

Mataimakin dai ya yanke wannan shawara ne domin yana son ya koma ya huta sannan kuma yafara koyar da kungiya a matsayin babban mai koyarwa ba mataimaki ba kamar yadda yasaba a lokutan baya.

Rui Faria yace yanzu lokaci yayi da zai fara cin gashin kansa na koyar da kungiya da kansa batare da Mourinho ba kuma wannan ma karamin ci gaba bane a rayuwarsa amma kuma zai je ya huta da yan uwa da iyalai kafin kuma yadawo fili.

Sannan ya nuna godiya ga Jose Mourinho bisa yadda da amincewa da yayi dashi tsawon shekaru 17 da suka dauka suna aiki tare wanda hakan yake nufin ba abune mai sauki ba rabuwa da Mourinho wanda ya amince dashi.

Yaci gaba da cewa yana godiya

 

Exit mobile version