Connect with us

LABARAI

Mataimakin Shugaban Hukumar NIS Ya Rasu

Published

on

Shugaban Hukumar shige da fici ta kasa Muhammad Babandede, ya sanar da mutuwar mataimakinsa, DCG Raymond Tonye Akrah Jaja ,wanda ya rasu ranar 9 ga Yuni na shekarar 2018, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Dan asalin Jihar Ribas, kafin rasuwarsa, DCG Jaja shi ne shugaban sashen kula da tsaron kan iyaka a shalkwatar hukumar NIS da ke Abuja.

DCG Jaja wanda aka haifa e ranar 11 ga watan Disamba 1960, ya halarci sananniyar Jami’a ta Nsukka, inda ya karanta kimiyyar siyasa. Ya fara aiki da Hukumar shige da fice ta kasa, a shekarar 1985 a mukamin mataimakin safurintanda. Ya halarci kwasa kwasakwasai na horarwa danagane da aikin shi, a nan cikin gida da kuma waje, cikin su har da makarantar horon manyan ma’aikatan Hukumar da take a Sokoto, da kuma cibiyar nazarin harkar tsaro da ke Jaji.

An kara ma shi girma zuwa mukamin mataimaki shugaban hukumar a shekarar 2017, bayan haka ne kuma aka mai da shi, saboda ya shugabanci wani sabon sashe wanda aka kirkiro don kula da tsaron kan iyakoki, mukamin da yake ya rasu a ranar 9 da watan Yuni 2018.

Sanarwar da jami’in yada labaran hukumar, DCI, Sunday James ya raba wa manema labarai, ta bayyana cewa za a rika  tunawa da DCG Jaja saboda mutum ne mai kamala, ga halaye masu kyau, da kuma biyayya ga dukkan dokokin da suka shafi aikin shi, sannan har ila yau mutum ne mai son sakin fuska.

Nana gaba kadan za a bayyana ranar da za a rufe shi. Ya mutum ya bar mata daya da kuma ‘ya’ya biyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: