Mataimakain Shugaban kasa Yomi Osinbanjo ya kaddamar da damar kulawa da l;afiyarc al’umma, wanda aka yi a dakin taro na fadar Shugaban kasa dake Abuja. Hukumar kula da kare ‘yancin kare masu amfani da kayayyaki, ya samu halartar masu ruwa da tsaki a bangaren kula da lafiya, wanda kuma ya hada da kungiyar Likitoci ta kasa.
PBoR wata hanya wadda take nuna dama ko kuma damarmakin da wanda yake amfani da kayayyakin, wani abu ne wanda dama ko kuma damarmakin da akwai su, da kuma asu abubuwa cikin tsarin mulki na shekarar 1999. Dokar kafa Hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki, sai kuma damar da yara a, dokar damar samun bayanai, da kuma dokar kula da lafiya ta kasa da dai sauran wasu dokokin.
PBoR Hukumar kare ‘yanci ko kuma damar da masu amfani da kayayyaki ce ta yi ta, sai kuma sauran wadanda suke da ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatar lafiya ta tarayya, saboda kare masu amfani da kayayyaki.
A lokacin shi bikin Mista Osinbajo ya bayyana cewar “ Yau mun dauki wani babban mataki, saboda tabbatar da an dauki wasu matakai na kulawa da damar da mutane suke da iata wajen kulawa da lafiyar su, wadanda ya dace a kula dasu wajen aiwatar dasu, da kuma kare su, wannan kuma ya kasance dolr ne saboda a halin da ake ciki babuwanda aka yi ma allurar da zata hana shi neman taimakon kulawa da lafiyar shi. Babban al’amarin shine jin dadin mu, sai kuma ko shekrau nawa aka sa ran zamu yi, wadannan kuma abin yan a da alaka ne bangaren lafiyar jiki yadda ake kulwa da ita.”
Da yake jawabi akan muhimmancin ita dokar a Nijeriya Mista Osinbanjo ya yi tsokaci a irin halin ko in kula wanda ‘yan Nijeriya suke ciki dangane da lafiyar su.
Ya bayyana cewar “Wani binciken da aka yi shekarar 2016 wanda PwC [Price Waterhouse] ya yi, ya bayyana cewar kashi 90 na wadanda suka amsa, suna da wata alaka da harkar kula da lafiya ta Nijeriya, ya yin da kuma kashi 80 da kuma fiye da kashi 70 gaba daya, sun danganta alakar su da ita da wasu kalmomi kamar mai taurin kai da kuma
tsoro’. Amma kuma sai ga shi kasa da kashi 20 shi al’amarin yadda ake kulawa da lafiya a Nijeriya, lalle wanka ya biya kudin sabulu, su kuma kuma kasa da kashi 10 sun ce a na kamanta gaskiya.