Bello Hamza" />

Matakai 10 na Samun Cikakkiyar Nasara A Harkar Kasuwanci

Samun nasara a harkar kasuwanci na bukatar aiki tukuru da naci saboda babu wani hanya mafi sauki na samun nasara a harkar kasuwanci ba tare da aiki tukuru ba.

Yawancin wadanda suka samu nasara a harkar kasuwanci da suka fuskanta na da labarai iri daya na hanyar da suka bi har suka kai ga samun nasarar. Da yawa daga cikin litattafan da ake rubuta wa na hanyoyin samun nasara a harkokin kasuwanci zaka samu suna magana a kan mahimman matakai iri daya ne na hanyar daya kamata mutum ya bi domin samun nasara.

Matukar son harkar kasuwancin da ka ke da dakewa a kan abin da ka ke fuskanta na daga cikin abubuwan da suka banbanta wadanda suka yi fice a harkar sana’a ko kasuwancin da suka fuskanta har suka samu kaiwa ga nasara, samun wadannan matakan na bukatar baiwa na musamman, ga wasu matakan da zai taimaka wajen samun nasarar ga mai bukatar yin fice a harkar kasuwancin daya zaba.

Son Abin Da Kake Yi.

Tsananin bukata da son sana’a ko kasuwancin da kake yi na daga cikin mahimman abin da ke habbaka harkar kasuwancin. Rashin son abin da aka ke yi yana dankwafar da kokarin da zaka yi wajen samun nasarar a bin da ka ke fuskanta, hakuri da dakewa na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da nasara a kan abin da aka fuskanta, nasara a kan mutum ko aikin ko kuma samun nasara a kan kanfanin gaba daya. Abraham Lincoln bai yi nasarar a kan abin daya fuskanta ba har sai daga kastshen rayuwarsa amma hakan bai sa ya cire tsammani ba ko ya cire rai ba.

Ka da Ka zuba dukka jarin ka lokaci daya.

Zuba jari gaba daya na da matukar hatsari kuma ba kasafai a ke samun nasara ba. a kwai labaran wadanda suka zuba dukkan abin da suka mallaka a matsayin jari lokaci daya kuma suka samu gaggarumin nasara amma ire-irensu basu da yawa, yin taka tsantsan na da mahimmanci musamman ga mai fara harkar kasuwanci, domin zaka iya jure karamar asara in har ka zuba kudade kadan, hakan kuma na zama kamar fagen daukan darasi a kan yadda zaka fuskanci harkar kasuwancin gaba daya.

Daukan darasi Daga Na Gaba.

Yawanci wadanda suka samu nasara a kasuwanci da suka samu kansu sun taba zama karkashin wani kafin su soma cin gashin kansu. Zama a karkashin wani shaharren dan kasuwa na ‘yan shekaru kafin ka fuskanci naka harkar yana da matukar nahimmanci. Zaka samu yanayin da zaka dauki darasi a kan kurakuran da aka gudanar ka kuma nemo hanyoyin kauce wa irin wadannan kurakuran nan gaba, ka samu wani da zai koya maka yadda zaka gudanar da kasuwancin kafin ka fukanci cin gashi kanka na matukar mahimmanci.

Ka Koyi Yadda zaka gabatar Da kanka.

Iya magana da gabatar da nau’in kasuwancin da kake gudanar wa na da matukar mahimmaci zai kuma daukaka harkar da kake yi na kasuwanci. Bunkasar kowanne irin kasuwanci ya ta’allaka ne daga wurin wanda ya kirkiro da na’uin kasuwancin. A kwai bukatar ka samu lokacin koyar yadda zaka tallata abin da ka kudirta a ba tare da tsoro ko shakka ba amma ka sani cewa abokin hurdan ka na kasuwanci shin ne ya fi mahimmanci a kowanne lokaci.

Gaggauta Dauka Mataki.

Kwararrarun ‘yan kasuwa masu kanfanoni na kan ci gaba ne a ko wanne lokaci basu da lokacin batawa na bin didigin duk abin daya faru domin hakan ba zai kai su ko ina ba, babu lokacin kananan bincike, aiki ne kawai dukkan ranakun mako a cikin awanni 24 na kowanne rana, babu hutu ko hutun rashin lafiya, kawai ka dauki bayanai sama sama na kowanne mataki da ka kai sai ka ci gaba ka kuma yi imani da kanka.

Ka Tsara Abin Da ka Ke Son Yi.

Ka zama mai karanta labarai da littafan mutane da suka samu nasara a harkokin kasuwanci da suka fuskanta, ka tsotsi dimbin ilimin da suka bayar na hanyoyin da suka bi har suka samu nasara, irin rubuce rubucen Stebe Jobs da na Shark Tank. Tsarin nasara a harkar kasuwanci ba yana nufin sai an rubuta littafi bane, ko da ‘yan shafi kadan ne matukar zai kunshij dukan abin da ka ke bukata na matakan samun nasarar ka a harkar kasuwancin.

Ka Samar wa Kanka Suna.

Kamar yadda wani masani mai suna Brandi Bennett ya yi bayani a shafinsa na intanet HostGator.com ya ce, ya na mahimmanci a samu shafi a kafar intanet domin tallata hajar ka, ko kai da kanka ka rinka zagaya wa domin tallata abin da ka ke iya yi domin masu bukata a kokarin wannan zagayen ka yi imani da abin da zaka iya yi tare da yin abin ba tare da wani shakka ba.

Ba a Makara Wajen Fara Harkar Kasuwanci.

‘Yan kasuwa da yawa da suka samu gaggarumin nasara sun fara harkar kasuwancin ne daga karshen rayuwar su kamar irinsu J. K. Rowling (Harry Potter author) da Julia Child (chef) da kuma Sam Walton (Wal-Mart) duk sun fara harkar da suka samu gaggarumin nasarar ne daga can cikin rayuwarsu, rashi farawa da wuri bai hana su samun nasarar ba. Dadewa a rayuwa na iya zama wani sinadarin da zai taimaka wajen samun nasarar da ake bukata. Dadewa a rayuwa na samar da wani hange na musamman da yaro ba zai iya samu ban a hangen nesa da zai taimaka wajen bunkasar harkar kasuwanci.

Samar Da Rukunin Abokan Tafiya.

A kwai bukatar samar da al’adan mutanen da zasu taimaka maka samun cikakkiyar nasara, abokan tafiyar kuma suna iya kasance wa a kowanne bangaren kasuwancin ka ba wai sai daga cikin bangarenka ba hakan zai taimaka maka bukasa tallan abin da kake fuskanta, samun abokan hurda daga kowanne bangaren zai matukar taimaka maka tallan harkar ka a kusan kyauta tare da tsimin kudaden shiga.

Ka Kula da Halayar ka.

Halin shugaban kanfani ko jagoran kasuwanci na da mahimmanci wajen nasara ko rashin nasarar harkar kasuwancin, lallaci da ragwanci da allubazaranci abubuwa ne da suke saurin cata sunan ka da harkar kasuwancin da kake gudanarwa. Sirrin nasara na tare da yin kurakurai tare da daukan nauyin kurakuran da aka yi da nufin ci gaba. Yarda da fuskantar kalubale kai tsaye ke mayar da mai harkar kasuwanci ya zama shugaba kai tsaye ba tare da samun cikkakiyar nasara. Fara harkar kasuwanci na da tsananin cin rai saboda haka sai an yi matukar daurewa.

Yayin da dukan wadannan matakan na da mahimmanci wajne samun nasara amma kula da kanka na da matukar mahimmanci. Motsa jiki da cin abin ci mai kyau tare da samun isasshen barci na da mahimmanci wajen samun nasarar wadannan matakan da muka zayyana.

Yawancin shugabannin manyan harkar kasuwanci da suka samu nasarar na da tsarin daya yi kama da juna wadanda suka hada da tashi daga barci da wuri dad a cin abinci dan kadan tare da hurda da abokai da lokuttan nishadi a kowanne mako..

Za a iya samun tsaiko wajen samun daidaito na wadannan matakan amma idan mutum ya kuduri aniyar samun nasara a kana bin daya sa a gaba zai iya samun nasara akan abin daya fuskanta. Girma da irin nasarar da za a iya samu wajen bunkasar kasuwanci ya danganta ne daga irin kokari zimmar da  mutum ya dauka a ciin zuciyarsa, haan ne zai karfafa da gaggauta samun nasarar da ake bukata.

 

Exit mobile version