Connect with us

Bincike

Matakai Da Yanayin Cutar Korona

Published

on

Assalatu Was Salami Ala Ashrafil Mursalin; Sayyiduna Muhammadu SAW. ‘Yan uwana mutanen Arewa Assalamu Alaikum.

Kwanakin baya, kusan sati biyu ke nan, na yi kokarin mun yi bidiyo na wayar wa da mutane kai game da annobar Korona da ta shigo cikin kasashenmu. Watakil a wancan lokacin saboda yadda muka yada abun, bai kai wajen hukumomin da suka dace ba, don haka ba a aiwatar da wadancan shawarwarin da muka bayar ba. Yanzu kuma ga shi mun shiga wani yanayi wanda ita wannan cutar ta shiga cikin “kasashen Arewa”.
A lokacin da muka ba da shawarwari inda an bi wadannan shawarwari, da watakil kawo yanzu Allah ya sanya an dakile ita wannan cuta (Cobid-19); wato ta yanke cudanya a tsakankanin al’umma, to sai ba a samu an yi hakan ba, saboda yadda yanayin tsaro da kuma halayyar zamantakewar mutanenmu.
To a wancan lokacin muna matakin farko (First stage) na wannan cuta, shi ne ake ce ma ‘Imported case’, wato ta kasance bakuwa ce da ta shigo mana daga wadansu kasashe. Yanzu kuma cutar ta zama ‘Resident case’, wato ana iya samun yaduwarta cikin al’umma (Community spread), ke nan yanzu cuta ce wadda ba bakuwa ba; tana cikin al’umma kuma al’ummar wannan mazauna su ne ke yada ta. Tun da har an shiga wannan mataki, akwai abubuwan da ya kamata a yi na fahimta wanda zai taimaka na kare ko rage yaduwar ita wannan cuta. Na farko abinda ya kamata a fahimta shi ne yanayi wajen guda biyar:
1. Yanayi na farko shi ne, wadanda ake ce ma ‘A symptomatic’. Su ne wadanda suna iya yin cutar har su kare ta ba tare da ta gwada alamar ma sun yi ta ba.
2.Akwai na biyu wadanda suke a ‘Mild case’. Su ne wadanda za su dan gwada alamar tari da atishawa; amma ba wata mura ba ce mai nauyi, za su iya warkewa ma ko da ta shan kwarar panadol guda biyu da bitamin C. Haka su ma ba su nuna alamarta.
3.Akwai ‘Moderate case’. Su ne wadanda za su yi zazzaɓi mai zafi, har su kwanta asibiti; sai sun sha magani sosai sun yi jinya kafin su warke.
4. Akwai ‘Sebere case’. Su ne wadanda ta kama musu hunhu, har ruwan ita wannan cutar ya fara dankarewa a jikin hunhu; numfashi yana wuyar fita. To irin wadannan sai an ba su magani sosai da sosai kafin a samu su warke.
5.Sai kuma na karshe da ake kira ‘Critical stage’. Wadannan su ne wadanda ta ci karfin huhunsu, ta daskare huhun; sun shiga wani yanayi da ake kira ‘Acute Respiratory Distress Syndrome’, wato suna cikin yanayi na tashin hankali, domin huhunsu ba shi budewa da rufewa; wani yanayi ne mai kama da an danna kan mutum cikin ruwa.
Wani karin bayani shi ne, yanayi guda uku daga cikin biyar din can ba su cutarwa sosai, saboda ana gane alama, sai a killace (kuarantine) mutum wuri guda. Yanayin da ya fi tashin hankali su ne yanayi guda biyu, su ne ‘A Symptomatic’ da kuma ‘Mild case’. Wato wadanda suka kasance karamar mura ce, don haka suna yada ta sosai a cikin al’umma ba a sani ba. To wadannan su ya kamata a kiyaye, mutane a farga a rinka a kula da wannan. Sannan, wannan cuta ce, kamar yadda na fadi a bidiyona ta farko cewar bakuwa ce da sai a yanzu ne ake fahimtarta sosai. To a yanzu binciken cutar ya nuna cewa yawancin wadanda take kamawa maza ne, amma ban ce mata ba ta kama su ko ba ta cutar da su ko ba ta kashe su ba, a’a! Sai dai mafi yawanci alkalumma sun nuna cewar kaso 70 cikin 100 ta fi galabaitar da maza a kan mata. Sannan kuma, wadanda ta fi galabaitarwa su ne masu manyan shekaru, daga dan shekara arba’in da biyu zuwa sama; ta fi galabaitar da su ta kuma fi saurin kashe su. Har wa yau dai ban ce ba ta kashe kananan yara ko samari ko wadanda suke masu kananan shekaru ba. Kowa tana iya kashewa, sai dai masu manyan shekaru kuma maza su ta fi yi wa illa! Bayan wadannan rukunin, akwai mutane wadanda da ma can suna dauke da wata cuta, kamar asthma ko wata kalar cutar huhu ta daban ko ciwon koda ko ma wani babban zazzaɓi… duk dai wata cuta wadda za ta rage garkuwar jikin dan’adam, to wannan cuta ta korona birus tana galabaitar da yawancin wadannan mutane.
Sannan yanzun alkalumma sun nuna, kamar yadda na sha fadi cewar, wannan wata sabuwar cuta ce wadda ba a san ta ba sosai, ana fahimtarta ne, mutane bakake, wato wadanda launin fatarsu yake da duhu tana cutar da su fiye da wadanda suka kasance farare. Shi kuma binciken ya nuna saboda mu masu launin bakar fata, muna da wani abu da ake ce wa ‘Melanin’, shi wannan sinadari yana kare mu daga zafin ko hasken rana, to wannan kariya da ya ke ba mu (bakar fata) yana sanya wa sai an zuki rana da yawa kafin ta jirkita shi zuwa bitamin D; to hakan sai ya janyo, saboda jikinmu ba shi da yawan bitamin D, tana yawan kashe bakaken mutane ko kuma a ce ta fi galabaitar da bakar fata a kan farare.
Sannan kuma a jiya, Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) sun wallafa cewar, wannan cuta ce wadda ta kasance wanda duk ya mutu ba shi yada ta. A da yadda ake tunanin cewa, ko mutum ya mutu yana yada ta, yanzu an fahimci ba haka ba ne. Da yake hanyoyin yaduwarta sun kasance majina da yawu da ruwan ido, ke nan wanda duk ya mutu in dai ba yana fitar da wani abu ne daga bakinsa ko hanci ko ido, to ba zai iya yada ta ba. Sai dai duk da haka, mutane a kiyaye! Ba hikima ba ne don an ce wanda ya mutu ba shi yada ta mutam ya je yana kama shi, domin wannan sabon abu ne, gobe ana iya samun wani bincike da zai nuna mamaci yana yada ta.
To shin ta ya ya za mu yi mu kare kanmu daga wannan cuta? Kamar yadda muka yi bayani a bidiyonmu na farko, yawan tsabta; wato wanke hannu da sabulu da ruwa, Insha’allahu yana rage ta, domin cuta ce da ke bin iska, wato idan ka yi magana ko atishawa ko ka yi tari, hakan shi ke fitar da kwayoyin cutar, kuma suna tsayawa a bisa iska kusan mintuna 45. To shi ya sa ake son a yawaita tsabta. Ga masu hali, ana iya sayen ‘Hand sanitiser’ a rinka shasshafe hannu ana gogewa a ko da wane lokaci. Sannan akwai takunkumin Bature yana da amfani guda biyu; yana kare kai, idan mutum yana da ita iska ba zai fita ba, ke nan ba zai goga ma wani ba. Haka kuma idan wani na da ita, kai ba za ka shaka ba. Idan babu halin sayen takunkumin a nemi hankici ko kyalle mai kauri (ba shara-shara ba) a yi amfani da shi, musamman idan za a fita waje a hadu da wasu mutane da ba a sani ba. Sannan kuma a yi kokari a raba mazaunin dattijai masu yawan shekaru da yara, domin su yara suna a rukunin ‘A Symptomatic’ ne, kamar yadda muka yi bayani a baya, don haka suna iya yada cutar amma su ba ta cutar da su ba, watakil ma har ta gama rayuwarta a cikin jikinsu, garkuwar jikinsu ta kashe ta, ba su nuna wata alama cewar suna dauke da ita. Wadannan su ne abubuwan da za mu iya yi a matsayinmu na al’umma don kare kanmu. A ɓangaren gwamnati kuma duk abinda ta ga za ta iya yi na wayar da kan al’umma domin kare su, za ta iya ci gaba da haka. Ina kuma janyo hankalin shugabanni don Allah a taimaka wa al’umma domin ana cikin halin rashi, a kasar nan ana cikin halin rashi, don haka a taimaka wa mutane, ga azumi ya kawo jiki, a rage musu wannan hali da suke ciki, abinda duk za a iya yi na taimakawa, a taimaka! Ba wai a nemi ƴan siyasa a ba su kudi ba, muna da Dagattai, muna da masu unguwanni, muna da Hakimai, muna da Limamai, muna da shuwagabannin coci-coci… akwai mutanen da aka sani a cikin al’umma wadanda suka kasance masu amana ne, to don Allah idan za a taimaka a nemi wadannan mutane masu amana ne a ba su, domin su taimaka su rarraba wa al’umma, ta haka za a sami takaita wahala. Sannan kuma ina kira ga masu hali, wato masu hannu da shuni, don Allah duk abinda suke da shi a taimaka. Kuma ina kira ga al’umma baki daya, ba wai dole sai kai Dangote ba ne ba, ko kai ka tara wani buhunhunan hatsi guda dari ko kana da wani makudan kudi, a’a, taimakon na kowa da kowa ne. Manzon Allah SAW ya ce
“Ba mumini ba ne wanda zai kwanta cikinsa cike, amma makwafcinsa yana jin yunwa.”
Saboda haka duk abinda kake da hali na taimaka ma wanda ba shi da shi, a taimaka. Muna dai kira duk wani mai hali na taimakawa ya yi kokari ya taimaka! Sannan ina kira ga ‘yan kasuwa don Allah don Annabi… kasashen yammaci da inda Kiristoci suke da yawa, za a ga cewa idan lokacin Kirsimeti ya zo ko lokacin Easter ko wani Thanksgibing ko wani babban al’amari wanda ya shafi addinin Kiristanci, sukan yi kokari su rage kudin kayan masarufi domin mutane su samu su saya, su ma su yi alfahari idan ranar Kirsimeti ko ranar Thanksgibing, to don Allah a taimaka. Allah ya kawo wannan musiba a gaɓar lokacin Ramadan, to a taimaka ma jama’a, a fito da kayan abinci, a taimaka a rage kudin kayan abinci, a taimaka yadda mutane za su sami damar yin azumi a cikin wadatuwa. Manzon Allah SAW ya ce, “Wanda duk ya ciyar da mai azumi, ko da da dan tsagin dabino ne, to yana da kamar ladar wanda ya yi azumi.”
Haka kuma Manzon Allah SAW ya ce, “Wanda duk ya yi aiki na alheri a lokacin azumi, Allah zai ruɓanya mishi ladar fiye da wasu lokuttan da ba na azumi ba.”
To don haka a yi amfani da damar wannan albarka (falala) da Allah ya kawo a taimaka ma mutane yadda za su amfanu, kuma mu duka mu amfanu da wannan. Kuma daga karshe don Allah in an ga wani kuskure a cikin wannan bidiyo da na yi, a yi kokari a gyara, wato a yi wata bidiyo, idan akwai wani babban bayani wanda ban kawo ba, ko kuma na yi kuskure, mutane don Allah a yi kokari a gyara a kuma yada wa mutane domin su fahimta.
Idan kuma abu ya yi daidai, don Allah a kara yadawa saboda mutane su fahimci halin da ake ciki. Ina godiya ga Allah kuma ina ma dukkan ƴan uwa wadanda ba su da lafiya a gida suke ko a asibiti, Allah ya ba su lafiya, wadanda suka riga mu gidan gaskiya Allah ya sa sun huta, mu da muke da rai Allah ya sa idan tamu ta zo mu cika da imani. Salamu Alaikum Wa RahmatulLah!

Fadila H Aliyu Kurfi da Hafiz Adamu Koza ne su ka samo wadannan bayanai su ka aiko daga Kano.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: