Matakai Hudu Game Da Kara Bude Kofar Kasar Sin Ga Duniya

Mahukuntan Kasar Sin sun kara mikewa haikan wajen bude kofofin kasar ga kasashen duniya don yaukaka zumuncin aiki da zai kai ga amfanar da juna.

Kamar yadda muka yi bayani a jaridarmu ta jiya Jumma’a, Shugaban Kasar Xi Jimping ya fito ya bayyana wa duniya kudororin da suka tasa a gaba don cimma muradun da suka sabbaba kara bude kofar kasar ga duniya.

Shugaban Sashen Hausa na Gidan Radiyon Kasar Sin, Malam Sanusi Chen, ya aiko mana da nazarin da ma’aikatansu ((Bello, Maryam, Kande, Zainab, Tasallah), suka yi kan kalaman shugaban kasan bisa wannan kudiri a yayin buxe taron shekarar 2018 na dandalin Boao na kasashen Nahiyar Asiya, a garin Boao na Lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da matakan samar da karin damammakin shiga kasuwanni, da kyautata muhallin zuba jari, da kara kare ikon mallakar fasaha, da kara shigo da kayayyakin kasashen waje cikin kasar Sin, don taimakawa yunkurin kara bude kofa a kasar.

Kasancewar a bana ake cika shekaru 40, tun bayan fara amfani da manufar bude kofa ga kasashen waje da gyare-gyare a kasar Sin. Cikin jawabin da ya gabatar mai taken “ bude kofa don samun walwala tare, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi don neman samun makoma mai haske”. Shugaba Xi Jinping ya takaita nasarori da fasahohin da kasar Sin ta samu bisa aiwatar da wannan manufa. A cewar shugaban, manufar da kasar Sin ta dauka a matsayin wani juyin-juya hali karo na 2 da ya taba abkuwa a kasar Sin, ta canza yanayin da kasar ke ciki, gami da yin tasiri ga duniya. Shugaba Xi ya ce, “Kasar Sin tana taka rawa a matsayin babbar kasa, yayin da take kokarin bude kofa ga duniya. Sa’an nan kasar ta samar da babbar gudunmowa wajen tinkarar wasu rikice-rikicen hada-hadar kudi, ta matakan da kasar ta dauka na shige da fice, da shiga cikin kungiyar WTO, gami da yunkurin gudanar da shirin ‘Ziri daya da hanya daya’. Cikin shekarun baya, kasar Sin ta kan samar da gudunmuwar da ta kai kashi 30% na karuwar tattalin arziki duniya. Hakan ya zama babban dalilin da ya sa tattalin arzikin duniya ke kara samun ci gaba, lamarin da ya taimakawa wanzar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.”

A halin yanzu, ana fuskantar babbar kwaskwarima a nan duniya, yayin da ake da tarin kalubale a gaban dukkanin bil Adama. Tabbas, sabbin fasahohi da kwaskwarima da aka yi ta fuskar masana’antu sun samar da damammaki ga kyautatuwar zaman takewar al’umma, haka kuma, sun haifar da kalubalen da ba a taba gani ba.

Mutane a wasu yankunan kasashe suna fama da yake-yake, wasu kuma suna fama da karancin abinci. Sauyin yanayi da kuma yaduwar cututtuka dukkansu manyan kabubaloli ne da ake fuskanta. Wadanda ke tarnaki ga hanyoyin samun ci gaba.

To me makomar bil Adama da na Asiya ke nufi?

Shugaba Xi ya amsa wadannan tambayoyi cikin jawabinsa, inda ya nuna hanyoyin samun ci gaba ga dukkanin bil Adama, wadanda suka hada da yin hadin gwiwa da kuma shimfida zaman lafiya da bude kofa ga kasashen waje da kuma yin kwaskwarima. Shugaba Xi ya ce, “Na yi kira da hadin gwiwar al’ummomin  duniya baki daya ta yadda zai dace da halin da muke ciki, wanda zai kuma tallafa wa al’ummomin kasa da kasa, tare da yin mu’amala da bangarori daban daban da abin ya shafa kan wannan batun. Ya zuwa yanzu, ina farin ciki matuka domin na samu amincewa daga kasashen duniya da dama da kuma al’ummominsu, har kiran ya shiga muhimmiyar takarda ta Majalisar Dinkin Duniya. A nan gaba kuma, ina fatan al’ummomin kasa da kasa za su yi hadin gwiwa domin tabbatar da dunkulewar kasashen duniya baki daya, ta yadda za a shimfida zaman lafiya da kuma neman ci gaban yankin Asiya, har ma da kasashen duniya cikin hadin gwiwa.”

A sa’i daya kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin girmama juna da nuna adalci da karfafa yin shawarwari da daukar nauyi cikin hadin gwiwa da fahimtar juna da cimma moriyar juna da kuma kiyaye muhalli domin gina makoma mai haske.

Babban taron wakilan ‘yan Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka kira a watan Oktoban bara ya sanar da cewa, tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin ya shiga wani sabon zamani. Xi Jinping ya bayyana cewa, a wannan sabon zamanin da ake ciki, jama’ar kasar Sin za su ci gaba da dogaro bisa karfin kansu, da yi wa kansu kwaskwarima, da inganta aikin kirkire-kirkire don kara samun ci gaba. Kana Sin za ta kara bude kofa ga waje, da inganta hadin gwiwa da ketare, a kokarin samun bunkasuwa tare da duniya baki daya, da bayar da babbar gudummawa ga ci gaban bil adama. Xi yana mai cewa, “Za mu tsaya tsayin daka wajen karfafa aikin yin kwaskwarima. Ko da mun gamu da wahalhalu, za mu kokarta don haye su, kuma manyan matsaloli ba za su tsorata mu ba. Za mu ci gaba da aikin har mu samu nasara. Bugu da kari, za mu bi manufar bude kofa ga waje don moriyar juna da samun nasara tare, za mu dora muhammanci kan aikin shige da fice, ta yadda za a iya kafa wani tsari bisa hadin kai a tsakanin yankunan teku da wadanda ke na tudu, da taimakawa juna a tsakanin kasashen da ke gabashi da yammacin duniya. Haka zakila, Sin za ta fitar da manufofin yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da niyyar kafa tasoshin yin ciniki maras shinge masu halayyar musamman na kasar Sin.”

Shugaba Xi ya kuma nanata cewa, komin matsayin da kasar Sin za ta samu wajen ci gabanta, ba za ta yi barazana ko nuna karfin iko akan sauran kasashe ba, haka kuma ba za ta sauya tsarin kasa da kasa da ake ciki yanzu ba. A Ko da yaushe, kasar Sin kasa ce da za ta ba da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaba da kiyaye tsarin duniya.

An dade ana yada jita-jita kan manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje. A cikin rahoton da aka bayar a yayin taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin manufar bude kofa ga kasashen waje. A cikin wannan jawabin da ya bayar a yayin taron dandalin Boao ma, ya sake jaddada cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta. Kana ya sanar da matakai hudu a wannan fanni, wadanda suka hada da kara sasaucin zuba jari a kasar Sin, da kyautata muhallin zuba jari, da kara kare ikon mallakar fasaha da kuma kara shigo da kaya daga ketare. Xi ya kara da cewa, “Za mu kara tabbatar da ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na duniya, da kara tabbatar da ikon mallakar kadara, da gudanar da ayyuka bisa dokoki, da sa kaimi ga yin takara da kin amincewa da babakere. A rabin farko na bana, za mu gama aikin gyara jerin sunayen kamfanonin da jarin da suka zuba ya ragu, da aiwatar da tsarin kula da kudin shiga na jama’ar kasar da sarrafa jerin sunayen kamfanonin da yawan kudin da suka samu ya ragu. A bana, za a sake kafa hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin, da kara gudanar da ayyuka bisa dokoki, da tsaurara hukunci ga masu aikata laifuffuka, da inganta rawar da dokoki ke takawa a wannan fanni. Za mu sa kaimi wajen ganin kamfanonin Sin da na kasashen waje sun yi mu’amala da hadin gwiwar fasahohi yadda ya kamata, da tabbatar da ikon mallakar fasaha na kamfanonin kasashen waje da suka zuba jari a kasar Sin. Hakazalika, muna fatan gwamnatocin kasashen waje za su kara tabbatar da ikon mallakar fasaha na kasar Sin.”

Exit mobile version