Connect with us

LABARAI

Matakan Da Hukumar FRSC Ta Dauka Game Dawowar Zirga-zirga Tsakanin Jihohi

Published

on

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ta shiyya ta 4, ta karfafa bukatar kiyaye ka’idar nan ta nisantar juna a lokacin da aka fara yin zirga-zirga a tsakankanin Jihohin kasar nan.
Cikin wata sanarwa da mataimakin Kwamandan hanya na hukumar, Terry Hoomlong, ya fitar a ranar Alhamis, tana cewa babban Kwamandan shiyya Jonas Agwu, ya yi wani taro da hukumomin tsaro.
Shiyyar ta Jos dai tana kunshe ne da Jihohin Filato, Benuwe da Jihar Nasarawa.
ACM Agwu ya ziyarci Kwamandan Bataliya ta 3 ta rundunar Sojin kasar nan da ke Jos, Manjo Janar Nuhu Angbazo, da kuma daraktan hukumar DSS na Jihar, Ibrahim Sale.
Baya ga bin ka’idar ta nisantar juna, hukumar ta FRSC ta sha alwashin magance matsalar masu daukan fasinjojin da suka wuce ka’ida a cikin motocinsu.
“Mun umurci jami’an hukumarmu masu aikin kai-komo a kan hanyoyi da su tabbatar dukkanin masu motoci da fasinjoji suna bin dokokin da aka gindaya.
Agwu ya yi kira ga sauran hukumomin da su samar da hadin kai domin kiyaye aukuwar hadurra da kuma inganta sha’anin tsaro.
A na shi jawabin, Angbazo ya kwatanta hukumar ta FRSC a matsayin jagora a kan abin da ya shafi kiyaye dokokin hanya a wannan nahiyar ta Afrika.
Ya kuma yi alkawarin yin aiki tareda hukumar domin tabbatar da samar da cikakken hadin kai a wannan yankin.
Sale na hukumar tsaron ta DSS ya bukaci hukumar da ta nemi hanyoyin magance yawan hadurra a daidai shatale-talen Polo da ke Jos.
Jami’in ya yi alkawarin ci gaba da bai wa hukumar ta FRSC cikakken hadin kai.
Advertisement

labarai