Matakan Da Za Kabi Don Fara Kiwon Tattabaru

Daga Abubakar Abba,

Kiwon tattabaru sanannen abu ne a Nijeriya, musamman a Arewacin kasar, ganin cewa, yara kanana su ma suna da sha’awar kiwata su.

Tabbabara na nuna alamar son zaman lafiya, inda hakan ya sa ake tashinsu a wasu bukuwan wanzar da zaman lafiya a duniya.

Da dan karamin jari za ka iya shiga cikin fannin an kuma fi saurin samun riba ga wanda ya rungumi fannin, ta hanyar yin amfani da kayan kiwatasu na zamani sabanin na gargajiya.

Mahimmancin Kiwonsu:

Daga watanni biyar zuwa shida sun fara yin kwai haka ba su da wata wahalar sarrafa wa a wajen kiwo, za ka iya kiwatasu a bayan dakinka, haka in sun kai kimanin kwanuka 18 sai su fara kyankyashe kwan.

Daga sati uku zuwa hudu za ka iya cin naman ‘ya’yan, in ka zuba jari kadan za ka samu riba mai yawa.

Fannin ya kasance yana samar da kudin shuga ga wadanda suka rungumi fannin a kasashe kamar kasashen Bangladesh da Indiya da Nijeriya da Pakistan da sauransu.

Tsawon Rayuwar Da Take Yi:

Ana kiwatasu ne namiji da mace suna kasance wa a tare, har zuwa iya tsawon rayuwarsu suna kuma shafe shekaru daga 12 zuwa 15 suna rayuwa, kuma namjin ne yake samo shuci don gina musu gida.

A kullum suke yin kwai kuma suna kai wa kimanin shekaru biyar, ana yi musu baye haka macen da kuma namijin, suna kyansar kwai, inda suke kai wa kimanin daga kwana 17 zuwa 18 suna kyankyasar kwai.

Har Ila yau, cikin ‘ya’yan tattabarun da aka kyankyashe, yana dauke da abincin da za su dinga ci har zuwa kwana hudu, inda mace ke ciyar da ‘ya’yan har zuwa kwanuka goma har zuwa lokacin da ‘ya’yan za su fara cin abinci da kansu sai sun bayan sun kai kwanuka 26.

Wajen Kwanansu :

Yana da kyau, ka samar musu da gurin kwana mai kyau ana so dakinsu da za a gina shi mai tsawo don ba su kariya daga kai harin, musamman muzuru, Kare da sauran dabbobi masu illa, haka, ka kuma tabbar da dakin na samun shigar wadatacciyar Iska ka kuma sa fitila a dakin.

Za ka iya gina dakin da Katako ko kuma ka yi da Kwali ko wacce Tattabara na bukatar sararin da ya kai kimanin tsawon mita 30 da kuma fadin mita 30 na waje haka yana da kyau a dinga tsaftace dakinsu, musamman sau biyu a wata ko kuma a kullum haka, ana son abincinsu da kuma ruwan shan su, kasance a kusa dadakinsu.

Ciyar Da Su Abinci :

Tattabaru sun fi cin alkama da masara da shinkafa da sauransu, ana kuma son mai kiwonsu ya tabbatar d ya aje nasu abincun su a kusa da dakinsu na kwana, ana son abincinsu ya kasance mai gina masu Niki, musamman don su girma da wuri da kuma samun karin lafiya .

Ana son mai kiwonsu ya tabbatar da tukunyarsu ta ruwansu na sha na kusa da dakinsu na kwana, hakka ana son ruwan ya kasance mai tsafta .

Lokacin Da Suke Fara Yin kwansu:

Macen tattabara na fara yin kwai ne in ta kai wata biyar zuwa shida, inda take yin kwan a duk bayan wata daya, haka macen da kuma namijin suke kyankyashe kwan daya bayan daya har Ila yau, suna kai wa kwanuka daga sha bakwai zuwa sha takwas suna kyankyashe kwayayen.

Exit mobile version