Daga Abubakar Abba,
Ana noma lemon zaki kusan ko ina a daukacin fadin duniyar nan, kuma ya kasance daya daga cikin kayan lambu da za ka iya shuka shi a dan karamin waje ko kuma a gidan gona, musamman idan yanayi na da kyau.
Har ila yau, lemon zaki na kunshe da sinadaran da ke kara lafiyar jikin dan’adam lafiya, haka ana iya shuka shi a kowane yanayi na kakar noma, musamman daga watan Afirilu zuwa watan Mayu har zuwa watan Disamba.
Yana da kyau, ga wanda zai rungumi noman lemon zaki ya tabbatar da ya samu ilimin shiga noman, musamman idan har yana son ya samu cin nasara.
1 Samun Wajen Da Ya Dace Don Shuka Shi:
Za ka iya farawa da dan kadan, sannan ka fadada daga baya ta hanyar sayen gona da za ta ci kimanin bishiyar lemon daga 40 zuwa 50.
Ya kamata ka tabbatar da kasar noman tana da kyau tare da sinadaran da suka kamata a cikinta, inda za ka iya gane hakan shi ne, lokacin da kake gyaran gonar haka ya kamata ka lura cewa, shin abin hawa zai iya shiga gonar a cikin sauki don dakon lemon da ya nuna don sayarwa.
2 Kasar Noman Da Ta Fi Dacewa A Dasa Lemon Zaki:
An fi son a dasa shi a kasar noman da ruwa zai fi shigarta sosai a cikin sauki kuma yin gwajin kasar noman na da kyau, don a tabbatar da cewa, tana da kyau a shuka lemon zakin ko kuma a’a.
- Yanayin Da Ya Dace A Shuka Lemon Zaki:
Lemon zaki ya fi saurin nuna a dausayi mai kyau, haka yana jure wa ko wanne irin yanayi.
- Nau’ukan Lemon Zaki:
Yana da kyau, ka zabo na’u’in da ya fi dacewa don dasawa, musamman domin samun riba mai yawa, saboda haka an fi son ka dasa wanda zai fi saurin girma.
- Yi Masa Ban Ruwa:
Kamar dai sauran kayan lambu, shi ma lemon zaki na da bukatar a yi masa ban ruwa, domin idan yana samun ruwa akai-akai, za a fi samun amfani mai yawa, haka kuma ya kan jurewa rashin samun ruwa.
- Yana Da Kyau Ka San Yadda Lemo Ke Girma Daga Irinsa :
Yana da kyau, ka san yadda lemon ke girma daga irinsa, an kuma fi yin hakan ne a lokacin damina, musamman ganin cewa, a lokacin ne aka fi samun wadataccen ruwan sama, ana kuma son ka dasa irin ya kai tsawon kimanin mita 1.2, ka kuma tabbatar da yana samun wadataccen hasken rana, ana kuma son ka dinga zuba masa taki a kalla sau daya a sati don ya yi saurin nuna.
- Zuba Takin Zamani:
Domin samun amfani mai yawa, kana iya zuba masa takin zamani, musamman don gudun ka da ya lalace bayan an dasa irinsa.
- Samar Wa Da Bishiyar Sarari:
Yana da kyau a samar wa bishiyoyin sarari, musamman don su dinga samun wadataccen hasken rana yadda za su yi saurin girma, haka ana son ka tabbatar da bishiyarsa ta kai sararin fadin kafa 12 zuwa 25 a tsakanin juna.
- Yadda Yakamata A Kula Da Bihiyar Lemon Zaki:
Yana da bukatar a kula da shi yadda ya kamata kamar dai sauran kayan lambu, musamman don a ba shi kariya daga kamuwa da cututtuka ko kwari kuma za a iya yin hakan ne, ta hanyar samar da maganin feshi da ya fi da cewa.
- Lokacin Da Ya Fi Dacewa A Debe Shi:
A bisa hakikanin gaskiya, bishiyar lemon zaki na kaiwa tsawon shekara daya kafin a fara diba, wanda ana gane hakan ne bayan da lemon ya fara faduwa da kansa, inda kuma sauran da suka nuna a jikin bishiyar za a iya cire su, haka an kiyasta cewa, ana iya cirar kimanin lemon zaki 50 a jikin bishiya daya.